Digestive System

A duk lokacin da halittu suka ci abinci kamar mutane da dabbobi, Digestive System shi ne injin da amfaninsa kawai shi ne markaɗa wannan abu da ya shigo ta yadda zai kasance mai amfani ga sashinan jikin mutum.

Sashinan Digestive System

Waɗannan kuma su ne sashinan da suka haɗa digestive system, kowanne sashi akwai muhimmin amfaninsa:

  • Mouth– abu na farko da ake yi shine tauna abinci yayin da ya shiga bakin mutum. A nan, duk girman abu zai farfashe ta yadda mutum zai iya haɗiya.
  • Pharynx – abu na gaba kuma shi ne haɗiya, wato bayan an gama taunawa sai haɗiya wanda shi ne zai ba da damar abincin shiga ciki.
  • Stomach – a wannan matakin ne abinci yake kai wa sa’o’i 4 ko fiye da haka a ciki, a inda wasu sashinan injin zasu fara gudanar da nasu markaɗen, wato enzymes
  • Small intestine – daga nan kuma za a turo shi ƙaramin hanji, a wannan matakin shi ma zai ƙara matse shi don a ware mafi amfani a tura shi sassan jikin mutum inda zai yi aiki, sauran kuma a turo su babban hanji
  • Large intestine – duk wanda aka turo babban hanji na nufin ba shi da wani amfani a jikin mutum, daga nan kuma ya zama bahaya.

Karanta:

Madogara

[1] Biology> Digestive System > References