Chromosome

Credit: University of California

Chromosome wasu ƙwayoyi ne a cikin cell waɗanda suka samu daga DNA. Bayanan da suke cikin chromosome su ke ba wa cell damar tsara siffar wannan halitta; yadda za ta kasance kamar yadda bayanan suka nuna a chromosome. Bayanan da suke cikin chromosome kuwa sun haɗa da tsarin jinsi, zubin halitta, siffa da makamantansu waɗanda suka samo asali daga DNA.

Bayani

  • A kowanne cell akwai chromosome
  • Kowane mutum yanada chromosome 46 a jikinsa waɗanda ya samu 23 daga wurin uwa, sauran 23 a wurin uba
  • Sauran halittu kuwa, kamar kare, yana da chromosome 78, kyanwa tana da 38
  • Masana sun jera chromosomes a jadawali daga 1 zuwa 22 a matsayin ɓarin X da Y, na 23 din shi ne X/Y; wanda shi ne amsa ta ƙarshe don gane jinsin halitta.
  • Ɓari biyu na chromosomes X da Y da su ake amfani wajen gane jinsi – XX shi ne mace, XY kuma namiji.

Karanta:

Madogara

[1] Biology> Chromosome > References