Cell

Cell ya kasance jigon rayuwa ne a jikin halittu. Masana kimiyya suka ce ya samu ne daga ruwa, wanda shi ne asalin samuwar rayuwa.

Bayani

  • Masanin kimiyyar halittu Robert Hooke ne ya fara gano jigon rayuwa cell a shekarar 1655, wanda hakan ya faru ne ta hanyar amfani da na’urar ganin ƙananan abubuwa, saboda yadda wannan ƙwaya ta kasance mai tsananin ƙanƙanta da ido ba ya iya ganinta ƙuru-ƙuru sai ta hanyar amfani da na’ura.
  • Masana kimiyyar da suka ba da gudummawarsu da nazariyyoyi sun haɗa da Theodor Schwann, da Matthias Schleiden, da Rudolf Virchow, da kuma Anton van Leeuwenhoek. Waɗannan masana kimiyya su suka gina nazariyyoyi masu muhimmanci a game da jigon rayuwa cell
  • Akwai aƙalla cells guda tiriliyan 37 a jikin mutum

A bincike-binciken an gano cewa wannan jigo na rayuwa ya kasance uba ga rayuwar kowacce halitta, don haka kowacce halitta sai da shi take iya rayuwa. An ƙara gano kaso 90% na jigon rayuwar ruwa ne, wanda hakan ke ƙara tabbatar cewa shi ma ya samo asali ne daga ruwa. Sannan ya kasance a kowane sashi na jikin halittu, duk inda aka samu saɓanin kasantuwarsa to babu rayuwa a wurin

Ire-iren Cell

  • Prokaryotic cells –duk da cells sun kasance ƙanana matuƙa, amma irin waɗannan sune mafiya ƙanana daga cikinsu. Sannan ba su da nucleus; wanda ya kasance akwati ne ga sinadaran ƙwayoyin halitta DNA.    
  • Eukaryotic cells –wannan kuma shi ne rukunin cell da yake da girma kuma yake da akwatin nucleus inda DNA ɗinsa yake.

Bambancin Prokaryotic da Eukaryotic Cells

BambanciProkaryotic CellsEukaryotic Cells
AsaliShekaru biliyan 3.5Shekaru biliyan 2
Nucleus01+
Chromosomes11+
Cytoskeleton10
MisaliBacteriaDabbobi, tsirrai…

Madogara

[1] Biology> Cell > References