Animals

Kowacce dabba akwai rukuninta, akwai jadawalin da ake ajiye ta. Haka nan kowane rukuni yana da sashe. Waɗannan rukunin tare da sashinansu su ne inda kowacce dabba take:

Mammals

Mammals su suka kasance manya daga cikin dukkan dabbobi. Su ke da ƙashin baya da kwarangwal mai tsari. A takaice dai a wannan rukunin ne mutum da sauran namun dawa suke. A nan akan samu dabbobi kamar zaki, giwa, damisa, zomo da sauransu.

Fish

A wannan rukuni duk wani kifi yake, inda akwai aƙalla nau’ukan kifaye 30,000 a duniya. Kifaye kamar tarwada, karfasa, shark da makamantansu.

Birds

Duk wani tsuntsu a wannan rukuni yake. Dukkan wani tsuntsu da ke yin ƙwai kuma ya ƙyanƙyashe yana wannan rukuni. Misali irinsu jimina, aku, kurciya, hafziya, mujiya da sauransu.

Reptiles

Reptiles su ne dabbobin da yawanci suke jan gindi, wato waɗanda suke tafiya a kwance, kamar ƙadangare, maciji, kada, hawainiya da sauransu

Amphibians

Duk da dabbobin da ke wannan rukuni suna kama da reptiles. A nan, waɗannan dabbobin yawancinsu suna tsatso ruwa ne daga jikinsu kamar kwado.

Insects

Waɗanann su ne ƙwari –kamar sauro, buzuzu, gizo, malam-buɗe-littafi da sauransu. Duk waɗannan halittun da ke wannan rukuni su ne wadanda ba su da ƙashin baya, wato waɗanda ake kira invertebrate.

Madogara

[1] Biology> Animals > References