Venus

Credit: NASA

Duniyar Venus ɗaya ce daga cikin duniyoyin Solar System, kuma ita ce mafi kusanci da rana bayan duniyar Mercury wacce ta kasance ta ɗaya a jadawali. Duniyar Venus tana kamancecniya da duniyar Earth sosai, yanayin ƙarfin maganaɗisonsu ma kusan ɗaya ne –sai dai bambanci kaɗan.

Bayani

Nauyi: kaso 82% na duniyar Earth

Faɗi: 12,104 km

Ƙarfin Maganaɗiso: 8.87 m/s^2

Yanayi: 465 °C (870 °F)

Tazarar da ke tsakaninta da rana: kilomita miliyan 108.2 million

Ƙarin Bayani

Saboda yadda duniyar Venus take da haske sannan ba ta kasance ɓoyayya ba, hakan ya sa ake iya hango ta daga duniyar Earth. Mutanen da suna ƙiran duniyar da “tauraruwar maraice” ko “tauraruwar safe”, saboda a waɗannan lokuta ne ake iya hango ta. Amma zuwan Galileo Galilei ya tabbatar cewa duniya ce mai zaman kanta.

A zamanin da ake kira Space Age; wato a shekarar 1957 da aka fara zuwa sararin samaniya har zuwa yanzu, Soviet Union ta tura jiragenta biyu Venera 9 da Venera 10 zuwa sararin samaniya a inda suka ɗauko hotunan duniyar Venus a shekarar 1975.

Madogara

[1] Astronomy > Venus > References