
Duniyar Uranus ita ce ta bakwai a Solar System, sannan ita ce duniya mafi ƙanƙanta a jerin duniyoyin da ke ƙawance da ita; duniyoyin Jupiter, da Saturn da Neptune. Sinadaran hydrogen da helium ne gundarin samuwar duniyar Uranus. Sannan tana saurin juyawa wanda ya fi na duniyar Earth, domin tana juyawa a cikin sa’o’i 17 ba kamar na duniyar Earth sa’o’I 24 ba.
Bayani
Nauyi: ta ninka duniyar Earth sau 14 a nauyi
Faɗi: 50,724 km
Zubbai: 13
Watanni: 27
Ƙarfin Maganaɗiso: 8.69 m/s^2
Yanayi: -216 C (-357 F)
Tazarar da ke tsakaninta da rana: kilomita biliyan 2.87
Ƙarin Bayani
Masani William Herschel ne ya gano duniyar Uranus a ranar 13 ga watan March, a shekarar 1781, ta hanyar amfani da na’urar hangen nesa. A shekarar 1986 hukumar NASA ta aika jirginta Voyager 2 duniyar Uranus ya ɗauko hotuna.
Madogara
[1] Astronomy > Uranus> References