Universe

Universe – ƙaunu. Dukkanin wasu duniyoyi, sama da kasa, sararin samaniya da duk wani mutum ya ke gani a wannan duniyar da ma wasu, duk suna cikin ƙaunu ne.

Ƙaunu ita ce gundarin samuwar komai da ke cikinta. Nazariyyar Big Bang ta haƙaito cewa ƙaunu ta wanzu kimanin shekaru biliyan 13 da da suka gabata sanadiyyar fashewar wata ƙwayar zarra.

Daga nan ƙaunu ta ci gaba da faɗaɗa har ta kawo wannan zamani, kuma har kullum tana ci gaba da faɗaɗa cikin saurin da ido ba zai iya ganewa ba.

Related Terms