
Triangulum wani gungun taurari ne da ya kasance ɗaya daga cikin gungunan taurarin da ke maƙwabtaka da juna –wato Local Group, a inda ya kasance gungun taurari na uku mafi girma a wannan matttarar gungunan taurarin bayan Milky Way da Andromeda.
Bayani
- A shekarar 1764 aka gano gungun taurari Triangulum
- Yana ɗauke da aƙalla taurari biliyan 40
- Ya ninka rana sau miliyan 50 a nauyi
- Tazarar da ke tsakaninsa da duniyar Earth ya kai gudun haske na shekara miliyan 3
Madogara
[1] Astronomy > Triangulum Galaxy > References