
A cikin watannin duniyar Saturn guda 53, Titan shi ne mafi girma a cikinsu kuma mafi girma na biyu a Solar System. Duniyar Saturn ta kasance daya daga cikin shahararrun duniyoyin Solar System saboda zubban da suka mata ƙawanya.
Bayani
Nauyi: ya ninka watan duniyar Earth sau 1.8 a nauyi
Faɗi: 5,149.4 km
Yanayi: – 40 °C (104 °F)
Ƙarin bayani
A shekarar 1655 masanin kimiyya Christiaan Huygens ya gano Titan ta hanyar amfani da ma’aunin hangen nesa. Wasu bincike da aka gudanar a wannan zamanin sun nuna cewa akwai tsaunuka a duniyar Titan. Masana sha sun tura jirage don gudanar da bincike a Titan, ciki har da jirgin hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta Turai; ESA, ta tura 1997 Cassini wanda ya dira a duniyar Saturn a shekarar 2004.
Madogara
[1] Astronomy > Titan > References