Supernova

Cresit: NASA

Supernova wani lamari ne da ke faruwa a duk lokacin da wani bijimin tauraro ya fashe. Irin waɗannan bijiman taurarin da suka kasance masu tsananin girma da nauyi da ƙarfin maganaɗiso, wanda dalilin hakan ne ke sa sinadaran jigon rayuwarsu ke saurin ƙarewa, sai rayuwarsu ta zo karshe. A wannan lokacin da sinadarin ya ƙare sai su fashe, wannan fashewa kuma ita ake kira supernova.

Birbidin da yayi saura, da kuzari da ƙarfin maganaɗison su za su ƙara bazuwa su ƙara wa wani abu ƙarfi kamar black hole da sauransu

Madogara

[1] Astronomy > Supernova > References