Sun

Credit: NASA

Rana ita ta samar da tsarin haskenta da ake kira Solar System. Ita ce take tsakiyar Solar System, yayinda duniyoyi ke kewaye da ita kuma suke zagaye ta. Tana da matuƙar nauyi da girma, ita ta ɗauke kusan kaso 99.9% na nauyin Solar System.

Bayani

Shekaru: biliyan 4.6

Nauyi: ta ninka duniyar Earth sau miliyan 1.3

Faɗi: 1,392,684 km

Zafi: 13,599,726 °C

  • Rana wata ƙaramar tauraruwa ce da ke rukunin Dwarf Stars
  • Sinadaran hydrogen da helium ne kan gaba wajen samar da ita
  • Akwai yiwuwar nan da shekaru biliyan 4 ta iya mutuwa sakamakon sinadaran jigonta da yake ƙarewa

Ƙarin Bayani

Hasken rana yana daukar aƙalla mintuna 8 da dakiku 20 ne kacal ya riske mu a duniyar Earth, a yayinda tazarar da ke tsakaninmu da rana ya kai kilomita miliyan 149.6. Sinadaran hydrogen kaso 74%, da helium 24% ne suka samar da rana. Sauran kaso 2% kuma sauran sinadarai ne kamar su oxygen.

Madogara

[1] Astronomy > Sun > References