Star

Credit: NASA

Da zaran dare yayi taurari suke fitowa kowa ya gansu, suna masu sheƙi da haske. Abunda mutum bai sani ba shi ne, tsakanin sa da waɗannan taurari akwai tazara mai nisan gaske, nisan da ake kwatanta shi da gudun haske.

Taurari sun samu ne ta hanyar markaden sinadaran hydrogen da helium, don haka suke da zafi da kuma haske. Hatta rana ita ma tauraruwa ce. Dukkansu suna rukunin abubuwan da suka ginu da sinadaran hydrogen da helium.  Akwai biliyoyin taurari a fadin ƙaunu a biliyoyin gungunansu.

Bayani

  • Taurari su kan yi miliyoyon shekaru kafin rayuwarsu ta zo ƙarshe
  • Da zaran tauraro ya mutu yana fara shawagi a gungunsu, har ta kai shi fadawa black hole
  • Rana ita ce tauraruwa mafi kusa da duniyar Earth, sai kuma Proxima Centauri; inda tazarar da ke tsakani ya kai kilomita tiriliyon 39.9
  • Tauraro ya kan iya kai shekaru biliyan 1 zuwa 10

Ire-iren Taurari

  • Giant Stars – a rukunin girman taurari, waɗannan su ne mafiya girma daga cikinsu. Giant Stars su kan iya girma har su iya kai wa girman Solar System, sai dai ba su kai ƙanana jimawa a duniya ba saboda sinadarinsu yana saurin ƙarewa saboda yanayin girmansu. Ba sa wuce shekaru biliyan 1 da ‘yan kai.
  • Dwarf Stars – waɗannan kuma su ne tsaka-tsakiya a rukunin girmansu, su ne waɗanda suka fi Giant Stars jimawa a duniya. Rana ma a cikin wannan rukunin take.
  • Neutron Stars – waɗannan su ne mafiya ƙanƙanta daga cikin taurari. Suna da matuƙar nauyi amma ba girma, faɗinsu ba ya wuce tsawon kilomita 20.

Madogara

[1] Astronomy > Stars > References