Spacecraft

Credit: SpaceX

Spacecraft sune jiragen da ake tafiya sararin samaniya a su. Akwai wani wuri a sama kaɗan da duniyarmu, bai wuce kilomita 100 da doron kasa ba da ake ƙira Karman Line, da zaran jiragen tafiye-tafiye sun je wurin za su fara fuskantar matsi saboda gurɓacewar iska, ko kuma rashinta, wanda hakan ya sa jiragen tafiye-tafiye ba sa iya wuce wannan wuri, don haka aka ƙirƙiro jirage tafiya sararin samaniya na musamman.

Jiragen Spacecraft sune suke iya wuce wannan wuri saboda ba a gina su bisa gudu akan iska ba ne. Da irin wannan jirgin Neil Armstrong tare da abokan tafiyarsa suka dira a kan wata a shekarar 1950.

Ire-iren Spacecraft

  • Crewed Spacecraft – waɗannan jiragen su suke daukar mutane su luluka da su sararin samaniya, wato da wadannan jiragen ake tafiya sararin samaniya.
  • Earth-Orbit Satellites duk wani tauraron Ɗan-Adam da ke zagaye duniyar Earth a wannan rukunin yake. Wato tauraron Ɗan-Adam ma a jirgi ake ɗaura shi domin ya rinƙa zagaye duniya.
  • Space Probe – waɗannan kuma su ne jiragen da ake zuba na’urori a cikinsu da kayan aiki a tura sararin samaniya domin gudanar da wani bincike
Credit: NASA

Jiragen Apollo 11 da Vostok 1 sune suka kafa babban tarihi; a inda Vostok 1 ya kasance jirgin da aka fara amfani da shi wajen tafiya sararin samaniya, sai Apollo 11 wanda ya ɗauki mutane zuwa duniyar wata.

Madogara

[1] Astronomy > Spacecraft > References