Solar System

Solar System – tsarin hasken rana da yake a sararin samaniya, wanda ke dauke da duniyoyi guda 8 ciki har da duniyarmu earth. Solar System shine gundarin tsarin hasken rana wanda ya kasance dauke da duniyoyi guda 8 da ke a kusa da gungun taurarinmu.

Solar System ya kasance a tsakiyar gungun taurari Milky Way, yana shafe shekaru miliyan 200 kafin ya gama zagaye a Milky Way. Wannan zagaye shi ake kira Galactic Year

A tsarin hasken ranarmu akwai tsarin duniyoyi wadanda ake kira inner planets kamar su: Mercury, Venus, Earth da Mars, sai kuma outer planets su Jupiter, Saturn, Uranus, da Neptune.

A cikin wadannan duniyoyi kawai duniyarmu ta Earth inda halittu masu rai suke rayuwa, sanadiyyar kasantuwar ruwa a cikinta.

A da duniyar Pluto ta kasance cikin jerin duniyoyi 9 da suke a Solar System, amma daga bisani a shekarar 2006 aka cire ta sakamakon tabbatar da binciken cewa ba ta cika sharuɗɗan zama duniya a karan-kanta ba.

Related Terms