Solar Mass

Solar Mass na nufin nauyin rana. Rana, wacce ta kasance gundarin samuwar Solar System, wacce duniyoyi ke zagayewa, wacce take ba wa duniyoyin haske; ta ninka duniyar earth a nauyi sau 333,000. Don haka da aka gano nauyin da rana ta ke da shi sai ake amfani da nauyin wajen gwajin nauyin wasu abubuwan, kamar tauraro ko wasu abubuwa a sararin samaniya, kamar yadda ake amfani da haske wajen auna nisan wuri ko tafiya.