Satellite

Satellite kan iya zama a bangarori biyu:

  1. Artificial Satellite – tauraron Ɗan-Adam. Wato wannan, ba tare da la’akari da sunan ba, na’ura ne mai zaman kansa da ake harba wa sararin samaniya don ya binciko wasu abubuwa, a inda gundarin aikinsa shine daukar hotuna da taimakawa wajen musayar sakonni.
  2. Natural Satellite – ya kan iya zama wata duniya a sararin samaniya, wata ko wani abu a sararin samaniya da ke zagaye wani abu. Misali kamar yadda wata yake zagaye duniyar earth, haka nan kamar yadda duniyoyi suke zagaye rana.