
Da Pluto ta kasance duniya mai zaman kanta, kafin a cire ta daga jerin duniyoyi a shekarar 2006. A shekarar 1930 Clyde Tombaugh ya gano ta a matsayin duniya, amma daga bisani da aka fahimci ba ta cika sharuddan kasantuwa duniya ba sai aka mayar da ita jerin Dwarf Planets.
Bayani
Nauyi: kaso 2% na duniyar Earth
Faɗi: 2,374 km
Watanni: 5
Yanayi: -229 °C (-380 °F)
Ƙarfin Maganaɗiso: 0.62 m/s^2
Tazarar da ke tsakaninta da rana: kilomita biliyan 5.9
Ƙarin Bayani
Duniyar Pluto tana zagaye rana a duk bayan shekaru 248. Tana da ƙanƙanta sosai don bata kai watan duniyar Earth girma ba. A shekrar 2006 hukumar NASA ta tura jirginta New Horizon don gudanar da bincike a duniyar Pluto, amma sai a shekarar 2015 jirgin ya fara kusantar duniyar. A nan ne ya ɗauki hotunan duniyar wanɗanda suka nuna asalin zubin halittarta.
Madogara
[1] Astronomy > Pluto > References