Pinwheel Galaxy

Credit: X-ray: NASA/CXC/SAO; IR & UV: NASA/JPL-Caltech; Optical: NASA/STScI

Pinwheel na ɗaya daga cikin manyan gungunan taurari da ke faɗin ƙaunu. Wannan gungun taurarin shi ne mafi kusa da duniyar Earth bayan gungun taurari Centaurus A. Yana da matukar girma da faɗi, ya ninka gungun taurari Milky Way sau biyu a girma.

Bayani

  • Masani Pierre Méchain ne ya gano gungun taurari Pinwheel a shekarar 1781.
  • Akwai akalla taurari tiriliyan 1 a cikinsa
  • Tazarar da ke tsakaninsa da duniyar Earth ya kai gudun haske na shekara miliyan 21
  • Nauyinsa ya ninka rana sau biliyan 3

Wani abu da ya bambanta gungun taurari Pinwheel da sauran shi ne ya kasance gungun taurari da bashi da Black Hole a tsakiyarsa, ba kamar sauran gungunan taurari da suke da ba.

Madogara

[1] Astronomy > Pinwheel Galaxy > References