Phobos

Credit: ESA

Photos ɗaya ne daga cikin watannin duniyar Mars. Duk da shi ne babba daga cikin su biyun (ɗayan Deimos), amma tsayinsa bai wuce kilomita 27 ba. Duka watannin duniyar Mars ɗin (Phobos da Deimos) suna zagaye duniyar ne cikin tsananin gudu.

Bayani

  • Kasar Soviet Union ta tura jirage biyu Phobos 1 da Phobos 2 don gudanar da bincike a Phobos, sai dai Phobos 1 bai bata a tafiya, shi kuma Phobos 2 ya dauko hoton watan a shekarar 1989
  • Haka nan jirgin Mariner 9 ma ya dauko hoton Phobos da Deimos a a shekarar 1971
  • Phobos ba shi da karfin maganaɗiso sannan a zubin halitta kuma yana kama da dankali.

Tarihin Phobos

Lokacin da Johannes Kepler ya yi nazarin cewa akwai watanni biyu a duniyar Mars ba a yarda da batunsa ba, saboda babu wata ƙwaƙƙwarar shaida da za ta tabbatar da hasashen nasa.

Amma a shekarar Asaph Hall masanin kimiyyar sararin samaniya ya gano watan Deimos, bayan kwanaki shida ya ƙara gano Phobos. A wannan lokacin ya sanya musu sunaye Phobos da Deimos; wadɗnda suka kasance sunayen gumakan Girka.

Madogara

[1] Astronomy > Phobos > References