Moon

Credit: NASA

Moon shi ne watan duniyar Earth. Wannan wata shi yake zagaye duniyar Earth kamar yadda ita ma take zagaye rana. Romawa suna ƙiran wannan wata da suna Luna, shi ne wata mafi girma na 5 a Solar System.

Bayani

  • Yana ɗaukar kwanaki kamar 27 kafin ya gama zagaye duniyar earth
  • Tazarar da ke tsakanin wata da duniyar earth kilomita 384,000 ne
  • Sau 6 matafiya sararin samaniya suna zuwa duniyar wata daga shekarar 1969 zuwa 1972
  • Jirgin kasar USSR ne ya fara zuwa duniyar wata a shekara 1959
  • Neil Armstrong shi ne mutum na farko da ya fara dira a kan wata a shekarar 1969
  • Sinadaran da suka samar da wata sune kamar haka: oxygen (60.0%), da silicon (16.5%), da iron (3.5%), da magnesium (3.5%), da titanium (1.0%)
  • Karfin maganaɗisonsa
  • Yana gudun kilomita 3,600 a duk sa’a guda don zagaye duniyar earth
  • Yanayi a duniyar wata ya na kai daga -173°C zuwa 127°C
Neil Armstrong a duniyar wata. Photo Credit: NASA

Ƙarin Bayani

Wata ya samu shekaru miliyan 60 bayan samuwar duniyar Earth. A wancen lokacin tazarar da ke tsakaninsa da duniyar Earth bai wuce kilomita 22,500 ba, amma a yau tazarar ta kai kilomita 384,000. Masana suka ce hakan ya faru ne sanadiyyar sake yin nisa da watan yake yi da duniyar Earth, inda suka ce duk shekara watan yana ƙara nisantar Earth da tazarar 3.8 cm kacal.

Madogara

[1] Astronomy > Moon > References