Milky Way

Credit: NASA

Milky Way shi ne gungun taurarinmu, shi ne matattarar taurari wanda idanuwanmu suke iya gani. A cikin biliyoyin gungunan taurarin da suke kaunu, Milky Way ne ya kasance mafi kusa da tsarin hasken ranarmu, inda duniyoyinmu suka kasantu.

Bayani

  • Nauyin gungun taurari Milky Way zai iya ninka na rana sau tiriiliyan 1.5
  • Akwai aƙalla duniyoyi biliyan 100 a Milky Way
  • An yi hasashen haɗewar gungunan taurari Milky Way da Andromeda nan da shekaru biliyan 4.5
  • Gungun taurari Milky Way shi ma yana juyawa
  • Gungun taurarin da ke maƙwabtaka da Milky Way shi ne Andromeda
  • Milky Way zai iya kai wa shekaru biliyan 13
  • Tazarar da ke tsakanin Milky Way da duniyar Earth ya kai gudun haske na shekaru 25

Ƙarin Bayani

Kamar dai kowane gungun taurari, a Milky Way ma akwai wani bijimin Black Hole da ake kira Sagittarius A*, da ya ninka rana sau miliyan 4.3 a nauyi. Ba wai shi kaɗai ba, akwai Black Hole sama da miliyan 100 a gungun taurari milky way.

Tarihin Milky Way

A zamanin baya mutane da sun ɗaga kawunansu sama sun ga taurari suna tunanin iyaka nan ne kawai faɗin ƙaunu, ba su san cewa dukkanin wani abu da mutum yake iya tunanin kasantuwarsa ta ɓangaren girma ko nauyi, ya kasance wani ƙaramin sashe ne a cikin ƙaunu ba. A shekarar 1610 masanin kimiyyar sararin samaniya Galileo Galilei ya hango dubunnan taurari a Milky Way, a nan ne masana suka yi hasashen cewa wannan wani sashe ne na taurari, wataƙila akwai makamantansa da dama.

A shekarar 1923 da masani Edwin Hubble ya tabbatar wa duniya kasantuwar Andromeda a matsayin gungun taurari, daga nan ne aka tabbatar cewa Milky Way ma gungun taurari ne mai zaman kansa, kawai ya kasance ne wanda mutane ke iya ganin taurarin da ke cikinsa.

Related Terms

Madogara

[1] Astronomy > Milky Way Galaxy > References