
Duniyar Mercury ita ce duniya mafi kusa da rana, ita ce ta farko a jadawali. Tana da ƙanƙanta matuƙa kuma tana da zafi sosai. Sinadaran karfe da dutse ne gundarin samuwar duniyar Mercury, don haka da zaran zafin rana ya dake ta sai ta ɗauki zafi.
Bayani
Nauyi: kaso 5% na nauyin duniyar Earth
Faɗi: 4,879 km
Yanayi: 427 °C zuwa -149 °C
Ƙarfin Maganaɗiso: 3.7 m/s^2
Tazarar da ke tsakaninta da rana: kilomita miliyan 57.9
Ƙarin Bayani
Duniyar Mercury tana gama zagaye rana a kwanaki 88, sannan ta juya a kwanaki 57. Wasu masanan tarihi suka ce masanan baya da suka rayu a 3000 B.C sun san duniyar Mercury, wasu kuwa suka ce Galileo ne ya fara gano ta.
Madogara
[1] Astronomy > Mercury > References