Kuiper Belt

Credit: NASA

Kuiper Belt wani wuri ne da ke sararin samaniya, yana waje-wajen Solar System a bayan matafiyar duniyar Neptune. Wannan wurin ya haɗa da sauran Dwarf Planets har da duniyar Pluto, akwai manyan abubuwan sararin samaniya da ke shawagi a wurin kamar su comet, asteroid da sauransu.

A shekarar 1930 da aka gano duniyar Pluto, masana suka yi hasashen kasantuwar wasu duniyoyi a bayan duniyar Pluto ɗin, amma ilimin wannan lokacin bai iya ba da damar gano wasu abubuwan ba. Sai a shekarar 1992 masana suka gano wasu abubuwa a bayan duniyar Neptune wanda suka haɗa da matafiyar duniyar Pluto, don haka a wannan lokacin aka samu damar gano wannan wuri Kuiper Belt.

Bayani

  • Akwai abubuwa a kalla miliyan 100 a Kuiper belt
  • An sanya mishi suna Kuiper belt saboda jinjina ga masanin kimiyyar sararin samaniya Gerard Kuiper

Madogara

[1] Astronomy > Kuiper Belt > References