
Jupiter ta kasance duniya mafi girma a Solar System. Ita ce ta biyar a jadawali. Duniyar Jupiter, ba ma girma kaɗai ba, tana da nauyin da ya ninka na duniyar Earth sau 318.
Bayani
Nauyi: ta ninka duniyar earth sau 318
Faɗi: 139,822 km
Yanayi: -145 °C (-234 °F)
Watanni: 79 zuwa 91
Ƙarfin Maganaɗiso: 24.8 m/s^2
Tazarar da ke tsakaninta da rana: kilomita miliyan 778.5 million
Ƙarin Bayani
Duniyar Jupiter da ta kasance mai girman gaske, masana suka ce da za ta ninka zuwa 50 na girman da take da shi yanzu, da za ta iya zama tauraruwa mai zaman kanta. Tana shafe sa’o’i 10 kacal domin ta gama juyawa, wanda hakan ke nufin kwana 1, kuma ta shafe shekaru 12 kafin ta gama zagaye rana.
Madogara
[1] Astronomy > Jupiter > References