Ganymede

Credit: NASA/JPL

Ckin watannin da ke duniyar Jupiter, Ganymede ya kasance mafi girma daga cikinsu kuma mafi girman wata a Solar System. Haka nan shi ne abu na 9 girma a Solar System. Haka nan duniyar Jupiter ita ce duniya mafi girma a Solar System.

Bayani

Nauyi: ya ninka watan duniyar Earth a nauyi sau 2 

Faɗi: 5,262.4 km

Yanayi: – 163 °C (325.4 °F)

Ƙarin bayani

Masanin kimiyyar sararin samaniya Galileo Galilei ne ya gano watan Ganymede a shekarar 1610. Bayan wannan Galileo ya gano watanni sun kai 3. Saboda girman wannan wata, da a ce rana yake zagayewa ba duniya, da zai iya zama duniya mai zaman kanshi, kuma ba za a lissafa shi a matsayin miskinan duniyoyi ba.

Ganymede yana shafe aƙalla kilomita 39,165 a duk sa’a guda a tafiyarsa ta zagaye duniyar Jupiter inda yake gamawa a kwanaki 7. Ke nan yana yin tafiyar kilomita 1,070,400 a kwanaki 7 don zagaye duniyar.

Madogara

[1] Astronomy > Ganymede > References