Galaxy

Galaxy na nufin gungun taurari, majalisa ko daba ce ta taurari. A gungun taurari daya akan iya samun biliyoyin taurari, haka nan akwai biliyoyin gungunan taurari a sararin samaniya.

Gungun taurarin da yake kusa da mu shine Milky Way, nan ne inda muke iya kallon taurarinsa idan mun daga kan da daddare.

Bayani

  • A yau binciken masana kimiyya ya tabbatar da cewa babban gungun taurari a fadin kaunu shine IC 1101, wanda ya kai gungun taurarinmu sau 50 a girma sannan ya sau 2,000 a nauyi.
  • Bayan wannan bincike ya kara nuna cewa a kalla tauraro daya ya fi rana girma sau 300,000.