Extrasolar Planet

Credit: NASA/JPL-Caltech

Extrasolar Planet ko exoplanet na nufin duk wata duniya da take wajen Solar System, wato take wajen rana ko ko ace ba ta tsarin hasken rana na Solar System, ita ake ƙira Extrasolar Planet.

Tabbas bayan duniyoyi 8 da suke a tsarin hasken rana, akwai wasu duniyoyin da suke waje, sannan akwai daruruwansu a sararin samaniya. Irin wadannan duniyoyi su ake kira Extrasolar Planet.

Insakulofediyar Britannica ta wallafa cewa an fara gano waɗannan duniyoyi ne a shekarar 1992, inda a yanzu haka aka tabbatar da kasantuwar sama da 4,000

Haka nan a gungun taurari Milky Way akwai exoplanets aƙalla 4,000, a inda sauran 5000 suke jiran a tabbatar da su.

Madogara

[1] Astronomy > Extrasolar Planet > References