Europa

NASA/JPL/DLR

Europa ya kasance ɗaya daga cikin watanni 79 da ke zagaye duniyar Jupiter, wacce ta kasance duniya mafi girma a Solar System. Masana suka ce da duniyar Jupiter za ta iya ninkawa zuwa 50 na girman da take da shi yanzu, da za ta iya zama tauraruwa mai zaman kanta.

Bayani

Nauyi: kaso 65% na watan duniyar Earth

Faɗi: 22.2 km

Yanayi: – 171°C (339 °F)

Ƙarin bayani

Masanin kimiyyar sararin samaniya Galileo Galilei ne ya gano wannan wata a shekarar 1610. Wannan wata da ke zagaye duniyar Jupiter yana kwanaki 3 ne kacal kafin ya gama zagaye ta, a inda tazarar da ke tsakanin farkon tafiyarsa da ƙarshenta ya kai kilomita 671,000.

  • Masana suka ce Europa zai iya kai wa aƙalla shekaru biliyan 4.5
  • Hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta kasar America; NASA, ce ta yi ruwa da tsaki wajen gudanar da bincike a Europa.

Madogara

[1] Astronomy > Europa > References