
Duniyar Earth ita ce duniya keɓaɓɓiya a duk faɗin ƙaunu, ita ce duniyar da halittu masu rai suke iya rayuwa a ciki. Ita ce duniya ta uku a jadawali bayan duniyoyin Mercury da Venus.
Bayani
Nauyi: 5.98 × 10^24 kg
Faɗi: 12,742 km
Yanayi: 15 °C (59 °F)
Watanni: 1
Ƙarfin Maganaɗiso: 9.81 m/s^2
Tazarar da ke tsakaninta da rana: kilomita miliyan 149.6
Ƙarin Bayani
Duniyar Earth tana zagaye rana a duk bayan kwanaki 365, sannan ta juya a duk bayan sa’o’i 24. Sannan tana gudun kilomita 1,600 a duk sa’a guda wajen juyawarta. A duniyar Earth ana samun sinadarai masu yawan gaske Haka nan ruwa ne ya mamaye kaso 70% na duniyar. Duniyar tana da wata guda ɗaya da ake ƙira Moon
Madogara
[1] Astronomy > Earth > References