Deimos

Credit: NASA

Kamar dai Phobos, haka nan Deimos ma ya kasance ɗaya daga cikin watannin duniyar Mars, sai dai Deimos ne kasance ƙarami daga cikinsu. Sannan Phobos shi ne ya fi kusa da duniyar Mars din, shi kuma Deimos yake ɗan nesa da ita kaɗan.

Bayani

  • Deimos yana ƙara nesantar duniyar Mars kamar yadda Moon yake yi wa duniyar Earth.
  • Haka nan jirgin Mariner 9 ma ya ɗauko hoton Phobos da Deimos a a shekarar 1971

Tarihin Deimos

Lokacin da Johannes Kepler ya yi nazarin cewa akwai watanni biyu a duniyar Mars ba a yarda da batunsa ba, saboda babu wata ƙwaƙƙwarar shaida da za ta tabbatar da hasashen nasa.

Amma a shekarar Asaph Hall masanin kimiyyar sararin samaniya ya gano watan Deimos, bayan kwanaki shida ya ƙara gano Phobos. A wannan lokacin ya sanya musu sunaye Phobos da Deimos; wadɗnda suka kasance sunayen gumakan Girka.

Madogara

[1] Astronomy > Deimos > References