Cosmology

Cosmology wani sashe ne na karatun kimiyyar sararin samaniya, inda ya ta’allaka da gano asali, tsari, ƙaddara da kuma hasashen abunda zai wanzu dangane da ƙaunu.

Wannan babban sashen ya ginu ne bisa lissafin tabbatar da abunda ya wuce a baya, nazariyyoyi da kuma hasashe.

Cikin manyan masana wannan sashe na kimiyya akwai Stephen Hawking, babban masanin kimiyya kuma marubuci wanda ya shahara a fagen ilimin asalin wanzuwar ƙaunu da hasashenta.