Comet

Credit: NASA

Comet wani irin dutsen ƙanƙara da ke shawagi a sararin samaniya. An fiye samun comets a Kuiper Belt, sannan suna matuƙar yin nesa da rana. A duk lokacin da zafin rana ya samu nasarar dukan comet sai wani ɓangarensa ya narke, sai ya samar da wani kullutu a jikinsa kamar wutsiya.

Masana tarihi suka ce tarihi ya nuna mutane sun kasance masu tsoron comets, suna tunanin shaidanu ne suke turo su don tarwatsa duniya musamman idan suka ga wulgawarsu da dare.

Akwai comets aƙalla 3576 waɗanda aka sani, kuma ana tunanin akwai biliyoyinsu a Oort Cloud da Kuiper Belt.

Tarihin Comet

A shekarar 1951 masanin kimiyyar sararin samaniya Gerand Kuiper ya gabatar da nazariyyarsa, wacce take nuna cewa za a iya samun wani faifai ɗauke da wasu duwatsun ƙanƙara a bayan duniyar Neptune. Wannan nazariyyar ta shi ta zo daidai don haka lamarin ya tabbata.

Madogara

[1] Astronomy > Comet > References