Centaurus A

Credit: NASA/ESA Hubble Space Telescope

Centaurus A, ko kuma NGC 5128 gungun taurari ne mafi kusa da duniyar Earth, a inda tazarar da ke tsakaninsa da duniyar bai wuce gudun haske na shekara miliyan 16 ba. Masanin kimiyya James Dunlop ne ya gano shi a shekarar 1826.

Bijimin Black Hole ɗin da ke wannan gungun taurari yana da nauyin da ya ninka nauyin rana sau miliyan 55. Wannan ke nuna ya fi bimijin Black Hole din da ke a gungun taurari Milky Way, domin shi ya ninka rana ne a nauyi sau miliyan 4 kacal.

Madogara

[1] Astronomy > Centauurus A > References