Big Bang

Big Bang Theory – nazariyyar kimiyya ce da ta kawo bayanin yadda ƙaunu ta wanzu. Nazariyyar Big Bang ta nuna yadda ƙaunu ta fara ta hanyar fashewar wata ƙwayar zarra da tayi sanadiyyar samuwar ƙaunun da abunda ke cikinta.

Nazariyyar Big Bang tayi bayanin yadda ƙaunu ta wanzu shekaru a ƙalla biliyan 13 da suka shude ta hanyar fashewar wannan ƙwayar zarra, daga nan komai ya samu kamar abubuwa, kuzari, da lokaci.

Wannan nazariyya ta ginu ne bisa fahimta da binciken manyan masana kimiyya tun daga shekarar 1912, lokacin da masanin kimiyyar sararin samaniya Vesto Slipher yayi nazarin yadda gungunan taurari suke gudana a sararin samaniya. Daga nan sai zuwa shekarar 1924, lokacin da masani Edwin Hubble ya gudanar da bincikensa kan gungun taurari da yanayin tazarar da ke tsakaninsu.

A shekarar 1927 masani Georges Lemaitre ya ƙara jaddada binciken wasu masana kan faɗaɗar ƙaunu. Dan haka daga bisani ya haƙaito cewa matukar dai ƙaunu tana faɗaɗa, to tabbas akwai wani lokaci da aka yi a baya inda take dunƙule (ƙwayar zarra).

Daga nan masana kimiyya suka ci gaba da faɗaɗa wannan bincike, kana daga bisani masani Fred Hoyle ya sanya wa nazariyyar suna Big Bang a shekarar 1949.