Asteroid

Credit: NASA

A shekarar 1801 wani masani da ake kira Giuseppe Piazzi ya fara gano Asteroid, wanda daga nan aka yi ta gano miliyoyinsu a faɗin ƙaunu. Wannan asteroid da Piazzi ya gano ya sanya masa suna Ceres, wanda ya kasance mafi girman asteroid a Solar System. Amma a lokacin shi ma bai san asteroid ba ne, ya ɗauka wata duniya ce, sai daga baya aka gano cewa Ceres ba duniya ba ce asteroid ne. Bayan shekara guda kuma wani masanin kimiyyar sararin samaniya mai suna William Herschel ya samar da sunan asteroid, wanda hakan ke nufin “kamar tauraro” –wato asteroid yana kama da tauraro.

Bayani

  • Ƙananan asteroid sune waɗanda tsayinsu bai wuce kilomita 1 ba, amma da dama daga cikinsu suna fin tsawon kilomita 100.
  • Masana sun yi hasashen yawan asteroid ɗin da aka sani za su kai 795,722, wadanda suke a Solar System kuma za su kai 600,000
  • Asteroid din da suke wajen Asteroid Belt su ake ƙira Trojan
  • Hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta turai, ESA , ta haƙaito cewa akwai aƙalla asteroid 10,000 da ke kusa da duniyar Earth
  • Ceres shi ne asteroid mafi girma, wanda tsayinsa ya kai kilomita 933; a inda shi kuma 1991 BA ya kasance asteroid mafi ƙanƙanta, bai wuce mita 6 ba.

Ƙarin Bayani

Yadda Asteroid yake shawagi a sararin samaniya. Photo Credit: NASA/JPL Caltech

Wani abu game da asteroid shi ne, ba su da nauyi; domin da za a haɗa dukkanin miliyoyin asteroid ɗin da ke a Asteroid Belt –wanda ya kasance gungun asteroid, da ba za su wuce kaso 4% na nauyin wata ba. Sai dai duk da haka tarihi ya nuna yadda wani asteroid ya daki duniyar earth shekaru miliyan 65 da suka gabata, wanda yayi sanadiyyar halakar dabbobin dinosaurs.

Ire-iren Asteroid

  • C-Type (carbon type) – waɗannan su ne asteroid din da suka gine da sinadarin carbon. Kaso 75% na asteroid din da aka sani a wannan rukunin suke.
  • S-Type (silicaceous type) – sannan kaso 17% asteroid din da aka sani sun ginu ne da sinadaran sillicates, irin waɗannan asteroid din kuma an fi samunsu a Asteroid Belt.
  • M-Type (metallic type) – waɗannan kuma sune waɗanda sua ginu da ƙarfen metal, nickel da kuma iron. 

Madogara

[1] Astronomy > Asteroid > References