Asteroid Belt

Credit: NASA/ESA

Asteroid Belt wani sarari ne a Solar System, wanda yake tsakanin matafiyar duniyar Mars da Jupiter. Wannan wuri yana ɗauke da duwatsu, asteroid da dwarf planets. Akwai miliyoyin asteroid a wannan yanki da ke sararin samaniya.

Bayani

  • An gano Asteroid Belt a shekarar 1801
  • Tsarin zubin halittarsa kamar faifai yake
  • Tazarar da ke tsakanin kowane asteroid yana kai wa kamar kilomita 965,606
  • Ceres shi ne asteroid mafi girma a Asteroid Belt, tsayinsa ya kai kilomita 950
  • Tazarar da ke tsakanin Asteroid Belt da duniyar Earth ya kai kilomita miliyan 329

Madogara

[1] Astronomy > Asteroid Belt > References