Andromeda Galaxy

Credit: NASA

Andromeda Galaxy yana ɗaya daga cikin gungun taurari da suka fi shahara. A rukunin gungun taurari da ke ƙawance da juna, wanda ake ƙira matattarar gungun taurari ko Local Group da ya ƙunshi gungunan taurari aƙalla 52, gungun taurari Andromeda shi ne ya fi kowane daga cikinsu girma. Sannan ya ninka gungun taurarinmu Milky Way girma sau biyu.

Bayani

  • Akwai tiriliyoyin taurari a gungun taurari Andromeda
  • An yi hasashen zai iya haɗewa da gungun taurari Milky Way nan da shekaru biliyan 4.5

Ƙarin Bayani

Kamar dai yawancin gungunan taurari, shi ma Andromeda yana ɗauke da wani Black Hole mafi girma a cikinsa da ya kai nauyin rana sau miliyan 100. Duk da akwai tazara mai nisan gaske tsakanin duniyar Earth da gungun taurari Andromeda, amma ana iya ganin wasu taurari da suke cikinsa idan dare yayi.

Tarihin Andromeda

Masana tarihi suka ce mutanen da ma’abota sanin kimiyyar sararin samaniya sun san gungun taurari Andromeda tun a karni na 10. Tun a wancen lokacin har zuwa shekarar 1855 lokacin da aka fara samun hoton Andromeda, masana ba su tabbatar da shi a matsayin gungun taurari ba. S wancen lokacin masana sun dauɗa wata ƙura ce da ake ƙira Nebula a gungun taurari Milky Way.

Amma a shekarar 1923 masanin kimiyyar sararin samaniya Edwin Hubble ya gabatar da hujjojinsa na kasantuwar Andromeda a matsayin gungun taurari, wanda hakan ya haɗa da la’akari da kasantuwar tauraro da yayi a cikinsa. Bayan haka ya ƙara auna tazarar da ke tsakanin duniyar earth da Andromeda, inda aka samu gudun haske na shekaru miliyan 2 da dubu 500.

Haka nan bayan an tabbatar da Andromeda a matsayin gungun taurari sakamakon cigaban kimiyya da fasaha, an kuma gano wasu duniyoyi a cikinsa.

Madogara

[1] Astronomy > Andromeda Galaxy > References