2

Yaya Siffofin Dusar Ƙanƙara Suke?

Tarin ƙanƙara da ta taru wuri guda ta cure sakamakon zubar dusar ƙanƙara idan ta dau wani lokaci sai ta daskare ba tare da narkewa ba ko da kuwa lokacin zafi ne.

Ita wannan gun-gun ƙanƙarar ta na samuwa ne a wasu yankuna da ake ƙira North Pole da South Pole ma’ana arewaci da kudancin duniya. Amma ita wannan tarin ƙanƙara a na samunta ne a wasu yankuna da suke da jerangiyar tsaunuka dake daf da sa. Misali: tsaunukan Himalayas da Andes.

Yaya tarin Ƙanƙara ke Samuwa?

Yayin da dusar ƙanƙara ta samu ko ta zuba a kan tsaunuka za ta cure ta koma kamar dutsi a saman waɗannan tsaunukan waɗanda ake ƙira hular ƙanƙara –Ice Cap.

Sannan tana ɗaukan ɗaruruwan shekaru kafin ta samar da wannan nau’in ƙanƙara ko da yake idan dusar ƙanƙara ta sauƙa a kan duwatsu sannan ta cure wuri guda za ta rinƙa gangarowa a hankali ta na lullube duwatsun ne har ta dinga samar da siffar hular.

Har ila yau ba wai sai a saman duwatsu kawai ake samun irin wannan siffa ba har akan dandariyar ƙasa akan iya samun wannan tarin ƙanƙarar sakamokon alaƙarsu da yankunan da dusar ƙanƙarar ke zuba. Misali ƙasar Turkey ana samun wannan suffa ta daskararriyar dusar ƙanƙara wanda har wani sani na teku da kogi na iya daskarewa.

Dusar ƙanƙara ba wai sai a yankuna da ke da tsananin sanyi ake samun ta ba har a yankunan da suke da kasancewar Hamada su ma suna iya samun wannan yanayi na ƙanƙara. Daga cikin ire-iren yankunan da suke da hamada amma akwai wanzuwar dusar ƙanƙara a wuraren sune:

  • Gobe Desert –wannan wani yanki ne da ke tsakanin manyan ƙasashe biyu wato China da Mongolia. Wani sashi daga arewacin China ya kasance tarin Hamada, sai kuma kudancin Mongolia
  • Atacama Desert –wannan yankin ya zaune ne a can nahiyar America ta kudu a cikin ƙasar Chile a daf da iyakar ƙasar da tekun Pacific, wanda shi wannan yankin ya kasance hamada amma ƙanƙara na zuba sa’i da lokaci.
  • Antarctica Desert –wannan hamadar ta kasance a nahiyar Antarctica a can maƙurar kudancin duniya, sannan ta kasan ce ɗaya daga cikin wurare mafi bushi a duniya duk da yanayin wurin ya kasance a lullube da ƙanƙara.

Waɗannan su ne kaɗan daga cikin yankuna masu matuƙar ƙanƙara amma kuma hamada ta kasance a yankin.

Ire-iren Dusar Ƙanƙara

Masana kimiyya dangane da samuwar ƙanƙara sun bayyana ire-iren ta da dama bisa la’akari da inda take, ga wasu daga cikin su

1. Cirque

Irin wannan dusar ko tarin ƙanƙarar ta na samuwa ne a magangarar dutse, wato idan ta zuba a saman tsolo-tsolon dutse idan ta taru tayi nauyi sai ta gangaro ƙasan dutsen ta ginu. Misalin irin waɗannan wurare za a iya kwatanta shi da irin dusar da ke zuba a arewacin kasar Afghanistan.

2. Ice Cap

Irin wannan tarin ƙanƙara na samuwa ne a mafi akasarin yankunan da ke da yawan tsaunuka masu matuƙar tsayi. Misali yankin da ake ƙira Caucasus wanda ya haɗa ƙasashen Azerbaijan, Georgia, da Armenia. Wadannan ƙasashe suna da irin wannan hula ta ƙanƙara saboda tsaunukan da ke wuraren.

Misali na biyu kuma shi ne yankin himaya da ya kasance yanki mafi tsayi saboda samuwar dutsen Everest na tsakanin iyakar India da Nepal har na da kasar Bhutan duk sun kasance suna da nau’ukan hular ƙanƙara a wuraren.

3. Ice Field

Wannan nau’in ƙanƙara ta fi shahara a sassan duniya saboda a na samun ta a mabambantan wurare, don tana zubowa ne a dandariyar ƙasa ba akan wani tsauni ba, ta kuma mamayi yanki mai yawan gaske.

4. Iceberg

Wannan ma wani nau’in siffa ce ta daskararriyar ƙanƙara wacce take ginuwa ta samar da wani siffa mai kama da gungumen dutse saboda curewa wuri guda da ta yi. Iceberg na samuwa ne yayin da dusar ƙanƙara ta taru wuri guda ta cure ta kuma ɗauki lokaci mai tsawo za ta ginu ta dawo kamar wani halittar tsaunin duwasu. Mafi akasarin irin wannan ana samun shi ne a wani yanki da ake ƙira Arctic Circle wanda wannan yankin ya ƙunshi ƙasashe da dama kamar su Norway, Sweden, Canada da dai sauran su. Cikin ire-iren yankunan nan ana iya samun Iceberg dalilin yawan zuban dusar ƙanƙara.

5. Calving

Wannan irin tarin ƙanƙarar ya kasance ana samun sa ne a daf da gaɓar kogi ko tabkin da ake samun zubar dusar ƙanƙara wanda daskararriyar ƙanƙarar za ta kasance kamar ita ne ma gaɓar bakin ruwan.

Madogara

[1] Wikipedia.org
[2] Duckster.com

Abdullahi Abubakar

Abdullahi Abubakar

I'm Abdullahi Abubakar from bajoga, gombe state. A former student in geography dept from fce,kano

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *