4

Fahimtar ‘Cryptography’ da Amfaninsa a Na’urori

cryptography

Ana yawan tambayar mene ne Cryptography kuma mene ne amfaninsa, musamman waɗanda ba su fiye shiga harkokin na’ura ba. Don haka a wannan rubutun za a fayyace mene ne cryptography da kuma amfaninsa a cikin na’ura.

Cryptography ya jima da kasantuwa a duniya, aƙalla a kan iya dire shi tun zamanin Sarkin Romawa Julius Caesar. Masana tarihi suka ce a wancen zamanin ana amfani da wani salo ne na ɓoye saƙo idan ana so a tura shi ga wasu, wato a ɓoye saƙon ko da a bayyane yake.

Karanta: Bayani kan Quantum Computer: Tsari, Amfani da Tasirinta a Duniyar Zamani

A lokacin da aka kasance ana isar da saƙo daga wani babban mutum zuwa wani –misali yadda sarakai ke isar da saƙo ta hanyar ba wa ‘yan’aikensu, sai suka samu wata fiƙira da za a iya aika saƙo zuwa ga wani ba tare da shi ɗan’aiken ya san abunda aka rubuta ba. Da wannan hikima masana suke isar da saƙonni.

To amma tayaya za a rubuta abu kuma shi ɗan’aiken bai san abunda aka rubuta ba?

Ana amfani da dabarun lissafi, da haruffa, da salon canje-canje don canja ma’anar wani harafi daga asalin yadda yake zuwa wani tsarin daban, ta yadda ba za a iya karanta asalin abunda aka rubuta ba. Misali, a kalmar flowdiary –sai aka mayar da ita yraidwolf –ke nan an canja mazaunan haruffa, na ƙarshe ya koma farko.

cryptography

A taƙaice, wannan shi ne salon cryptography da kuma shi ɗin kansa.

Mene ne Amfanin Cryptography?

Kamar yadda aka karanta bayani a taƙaice game da wannan fiƙira, cryptography ba wani abu ba ne illa hikima ta ɓoye bayanai a wannan zamanin kuma a cikin na’urori. Misali idan mutum yana so ya ɓoye wasu muhimman bayanansa, kamar lambobin sirri, sai ya ɗauki duk wani salon da yake so tunda akwai su da dama, ko kuma ya ƙirƙiri nashi da kansa ya ɓoye bayanansa. Misali;

Asalin bayanai: 08077

Ɓoye bayanai: 77080

Salon Ɓoye Bayanai

An kasance ana amfani da salo kala-kala ana ɓoye bayanai da su, sannan akwai salo kala-kala don bayyana bayanai –wato duk bayanin da aka ɓoye sai an samu salon da zai bayyana shi, misali;

Bayani: Flowdiary

Salon ɓoye bayani: shifting cipher

Ɓoyayyen bayani: gmpxehbsz

A wannan salon an ga yadda aka matsar da duk wani harafi zuwa matakin ɗan’uwansa kuma makwabcinsa.

A na’uroron zamani ana amfani da salon cryptography wajen ɓoye bayanai, kamar lambobin tsaro, muhimman bayanai da makamantansu. A ɓangaren gine-ginen manhajoji, shafuka ko rumbun bayanai, ana amfani da wasu salo don ɓoye bayanai ta hanyar amfani da tsare-tsaren na’ura kamar PHP da makamantansu.

Haka nan akwai dabaru kala-kala da ake amfani da su wajen ɓoye bayanai da bayyana su kamar wani salo na base64_encode a PHP Programming;

Madogara:

[1] Wikipedia.org

[2] Kaspersky.com

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

  1. Allah ya kara basira da daukaka… mun gode da wannan gagarumar gudumawa da FLOWDIARY take bayarwa ga al’umar arewa dama Nigeria gabadaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *