1

Me Ake Buƙata Don Zuwa Duniyar Wata?

Haƙiƙa tafiya sararin samaniya ba ta kasance tafiya mai sauƙi ba, wanda daga cikinta ne ake samun tafiya zuwa duniyar wata –wato Moon.

Duk da ya danganta ga inda aka tashi, amma dai abunda mutum ya iya sani shi ne ana tafiya wannan duniyar –saboda yadda ake ji a bakin wasu ko karanta maƙaloli a kai.

Tafiya sararin samaniya tafiya ce da take da matuƙar hatsari don ba a san abunda za a tarar a inda za a je ba, ga kuma tarin ƙalubalai waɗanda kan iya zama masu cutarwa ga matafiya. Don wannan dalili ya kasance ba kowa ba ne yake mafarkin tafiya sararin samaniya ballantana wata duniya daban.

A game da tafiya duniyar wata, tabbas mutanen duniya sun ji labari kuma sun karanta cewa an taɓa zuwa wannan duniya, kuma masani Neil Armstrong ne ya fara dira a kan duniyar. Wannan gagaruwar nasara ta kewaye duniya inda mutane da dama suke mamaki, wasu ma kan ɗauka labarun ƙanzon kurege ne kawai.

Da gaske ana zuwa duniyar wata?

Ba sau ɗaya ko sau biyu masana suke zuwa duniyar wata ba, abunda dai duniya ta sani shi ne duniyar wata ta kasance kamar wani wuri da matafiya sararin samaniya ke zuwa don gudanar da bincike.

A shekarar 1959 ƙasar Soviet Union ta aika jirginta duniyar wata, a inda shekarar ta kasance a tarihin duniya –shekarar da aka fara dira a kan duniyar wata. Hakanan a shekarar 1969 ma ƙasar America ta tura jirginta don gudanar da bincike a kan duniyar. Bayan nan sai shekarar 1972, sai 1976, sai kuma 2013.

Yaya duniyar wata take?

Duniyar wata ta kasance kamar wata duniya mai zaman kanta –sai dai ba za ta taɓa zama hakan ba, don ta kasance duniyar da take zagaye wata duniya; wato natural satellite. Duniyar wata tana zagaye duniyar Earth, a inda kuma duniyar Earth din ta ninka duniyar wata sau 3 a girma.

 • Ƙarfin maganaɗisonta ya kai: 1.62 m/s^²
 • Yanayi na zafi ko sanyi:  -173°C zuwa 127°C
 •  

Me ake buƙata don zuwa duniyar?

Masana, musamman waɗanda suke aiki a manyan ƙungiyoyin duniya ko hukumomin tafiya sararin samaniya; suna ba da wasu muhimman matakai da ya kamata matafiyansu su tabbatar sun cika sharuɗɗan kafin tafiya sararin samaniya.

A wannan rubutun kuma za a karanta waɗanne matakai ne ake bi don tafiya duniyar wata, me ake buƙata kuma me ya kamata a yi.

1. Fahimtar Sararin Samaniya

Dole matafiya su karanci me sararin samaniya ta ƙunsa; yaya take, ya yanayin tafiya a sama yake da makamantansu.

2. Sanin Duniyar Wata da Musabbabin Tafiyar

Bayan karantar sararin samaniya, dole matafiya su san yaya duniyar wata take, ya yanayinta yake, mene ne a duniyar, hakanan kuma mene ne musabbabin tafiyar.

Masana sun kasance masu aika jiragen sararin samaniya zuwa wata duniya ko sararin samaniya don gudanar da bincike game da yanayin yadda tsarin wannan wuri yake kafin su isa. Wannan yake nuna cewa haƙiƙa akwai buƙatar sanin wurin da za a je kafin a je ɗin.

3. Dacewar Kayayyakin Rayuwa da Guziri

Ba kowanne abu ba ne mai amfani zai kasance mai amfani a yadda yake a wata duniya. Wasu abubuwan ba za su kasance masu amfani a sararin samaniya ba, duba da yadda yanayi da tsaruka suka canja a can.

Haka nan game da guzuri, a sararin samaniya ba kowanne irin abinci ake zuwa da shi ba. Matafiyan suka ce ana zuwa bushashshen nama ne, da wasu abincin da ba a buƙatar dafa su ko waɗanda za su lalace.

4. Jagoran Tafiya

Jagoran tafiya shi ne wanda ya ɗauki nauyin wannan tafiya. Misali cibiyar bincike da hulɗar sararin samaniya ta America –wato NASA, da kuma ta Turai –wato ESA; su kan harba jirage zuwa duniyar wata da kuma sauran wurare a sararin samaniya.

A wannan matakin, wannan hukuma ko cibiyar bincike da ta kasance mai hulɗa da sararin samaniya ita za ta ɗauki nauyin tafiya zuwa duniyar wata, ke nan ita ke da alhakin samar da duk wani abunda matafiya za su buƙata.

Wataƙila zuwa nan gaba a iya samun wani jirgi da za a harba daga Nigeria zuwa duniyar wata, a inda kuma za a samu matafiyan da za su je.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and writer. I am the founder of Flowdiary.

One Comment

 1. Wonderful goods from you, man. I’ve understand your stuff previous to and you
  are just extremely magnificent. I actually like what you have acquired here, certainly like what
  you are saying and the way in which you say it. You make it
  entertaining and you still care for to keep it sensible.
  I can’t wait to read far more from you. This is really a terrific website.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *