5

Sararin Samaniya: Abubuwa 5 Da Ke Ba Wa Kowa Al’ajabi A Ƙaunu

Ƙaunu –wato universe ta ƙunshi abubuwa masu ban-mamaki da dama, amma daga cikinsu akwai wasu da suke da wasu abubuwa masu matuƙar ban-al’ajabi.

A wannan rubutun za a ga wasu daga cikin matuƙar ban-mamakin, wanda suka haɗa da:

1. Guguwar Shekaru 186

A duniyar Jupiter an taɓa yin wata fitinanniyar guguwa mai ban-tsoro, wacce kuma ba a taɓa gani ko jin labarin irin ta ba. Masana suka ce guguwar ta shafe shekaru 186 tana wakana a wannan duniyar, inda wani masani mai suna Giovanni Cassini ya fara gano hakan a shekakar 1665. Amma wasu masanan suka ce guguwar ta wakana ne a shekaru 356 –wato daga shekarar 1665 zuwa 1713.

2. Dutsen Zinare

Asteroid wani dutse ne da ke shawagi a sararin samaniya, musamman a matattararsa da ake ƙira Asteroid Belt. Haka nan yana yawo a duk wani wuri da zai iya zuwa a sararin samaniya. Abu mafi ban-mamaki shi ne akwai irin wannan dutsen wanda ya kasance na zinare ne zalla. Masana suka ce wannan Asteroid wanda ya kasance dutsen zinare mai suna Psyche 16 zai iya azurta kowa a duniyar Earth.

3. Duniyar Lu’u-Lu’u

Wata duniya da ke ƙaunu da ta kasance ta lu’u-lu’u zalla tana ƙara ba wa mutane mamaki kullum. A Solar System wasu duniyoyi sun samu daga sinadaran hydrogen, da helium, da gas da makamantansu, amma ita wannan duniya mai suna 55 Cancri e babu abunda ta ƙunsa sai lu’u-lu’u zalla. Shin yaya duniyar za ta kasance saboda girman wannan arziƙin?

4. Duniyar Rayuwa

A kaf faɗin ƙaunu babu wata duniya da ake rayuwa a cikinta face duniyar Earth. Ita ce duniyar da aka tabbatar da halittu suna rayuwa a cikinta. Ita ce duniyar da kominta yake daidai; zafi ko sanyi. Haka nan ita ce duniyar da ake ruwan sama.

Haƙiƙa wannan tsarin yana ba wa mutane mamaki musamman idan suka ji cewa ai duniyar Earth ce kaɗai inda ake rayuwa a halin yanzu, duk da masana suna ƙoƙarin gano wasu wurare da za a iya rayuwa bayan wannan duniyar, kamar binciken da masana ke yi a duniyar Mars.

5. Mafi girman girma, yawan yawa da nisan nisa

Wataƙila ido bai taɓa ganin wani abu mafi girman girma, ko mafi yawan yawa, ko mafi nisan nisa ba. Haka nan ko a tunani wani bai taɓa hakaito yadda wasu abubuwa suka kasance masu waɗannan siffofi ba. Amma dai a ƙaunu, fasalta waɗannan siffofin sun wuce tunanin mutum ma.

Mene ne mafi girman girma?

A duk lokacin da aka zo maganar girma, to ƙaunu da kanta ce take amsa wannan suna. Girman ƙaunu ne tunanin mai tunani ba ya ita haƙaitowa. Girman ƙaunu ne wanda ya wuce a misalta ko kwatanta shi da wani abu. Haƙiƙa ƙaunu ita ce mafi girman girma a duk wani batu da za a iya kawowa a tunanin mai tunani.

Mene ne mafi yawan yawa?

A kan iya samun abu mafi yawa, wanda yawansa ya kan wuce mizani ko ma’auni. Wasu suka ce ƙasa ce ta fi komai yawa, wasu kuwa suka ce ruwa ne, da dai makamantansu. Amma dai gane haƙiƙanin hakan ya danganta ga abunda mutum ya fi yarda da shi.

Ƙasa ko ruwa sun kasantu ne kawai a wannan duniyar ba a faɗin ƙaunu gaba ɗayanta ba. Amma idan aka zo maganar taurari kuwa, to masana suka ce haƙiƙa suna da yawan gaske, ko da ba za su iya zama mafiya yawan yawa ba.

A faɗin ƙaunu akwai gungunan taurari bila’adadin; inda kowanne gungun taurari ya ƙunshi biliyoyin taurari, wani gungun ma tiriliyoyi ya ƙunsa. Shin taurari –waɗanda ba su da iyaka a faɗin ƙaunu kan iya zama mafiya yawan yawa?

Mene ne mafi nisan nisa?

Da an zo batun nisa, wasu kan zubar da gwiwa idan suka ji adadin shekarun da za a iya ɗauka kafin a isa wani wuri. Duba da yadda wurare ke da nisa ne ya sa masana suka samar da dabarar yin amfani da haske wajen aune-aune. Misali, haske ya kasance abu mafi gudu a duk faɗin ƙaunu, don yana gudun kilomita 300,000 daƙiƙa guda –wato 300,000km/s. Ga jadawalin yadda gudun haske –wato speed of light yake:

Jadawalin Gudun Haske

gJerin LokutaTazara
1Light-second300,000km
2Light-minute18m km
3Light-hour1.07bn km
4Light-day25bn km
5Light-year9.46tr km
Nazarin Wikipedia.org, Space.com

Idan aka yi duba da duk waɗannan, za a fahimci cewa hakika haske yana da gudu, don haka ne ake amfani da shi wajen auna nisan tafiya. To amma duk da wannan tsananin gudun nashi, masana suka ce sai ya shafe shekaru biliyan 13.26 yana gudu kafin ya isa wani gungun taurari mai suna MACS0647-JD, wanda shi ne ya kasance mafi nisan wuri a ƙaunu.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and writer. I am the founder of Flowdiary.

5 Comments

  1. Gaskiya kana matukar kokari Mohiddeen, wannan shi muka rasa tun duniya na barci a arewacin Najeriya.

    Na matukar jinjina maka kwarai da gaske. Rubutu akan tech, history da science akwa wuya. Allah ya taimaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *