3

Ko Yaya Madatsa da ‘Yan Damfara Ke Samun Bayanan Mutane?

Bayanan sirrin mutum sun kasance ɓoyayyu a wurinsa, haƙiƙa samun su yana da matuƙar wahala. Amma duk da haka wasu su kan yi mamaki idan suka ji wasu madatsa –wato ma’abota hacking ko ‘yan damfara sun samu waɗannan bayanan sirrin.

Akwai hanyoyi da dama da ‘yan damfara suke samun bayanan mutum, misali samun bayanansa na banki ko wani asusunsa don gurɓata su ko yin amfani da su don damfarar sa.

Masana suka ce daga cikin dalilan samun bayanan mutum akwai sakaci; wato mutane ba su kasance masu damuwa da ɓoye bayanansu na sirri yadda ya kamata ba, su kan bayyana su a kusan ko’ina. Don haka wannan sai ya kasance dalili na farko da ke sa a birkita asusun mutum –mafi yawancin lokuta ba tare da saninsa ba.

Amma wasu daga cikin hanyoyin da madatsa da ‘yan damfara kan bi don samun bayanan mutum sun haɗa da:

1. Bibiyar Mutum

‘Yan damfara su kan bibiyi mutum don su gano wasu abubuwa dangane da shi waɗanda suka haɗa da bayanansa na sirri. Sakamakon yadda hanyoyin bibiyar mutum suka zama ruwan dare a wannan zamanin, samun bayanansa bai kasance aiki mai wahala ba. A kan bibiyi mutum a dandulan sada zumunta, a rinƙa kula da duk wani motsinsa da abubuwan da yake yaɗawa.

Shawara: a kula da bayyana manyan bayanan sirri!

2. Gano Kuskuren Mutum

Duk da kowa yana aikata kuskure a kullum, amma ‘yan damfara ko madatsa suna amfani da wannan kuskuren a matsayin wata dama don cutar da mutum. A nan, ko da karamin kuskure mutum ya aikata sai ya zama wata hanyar da wadannan macuta za su samu dama a kansa.

Akwai wasu kura-kuran da mutane kan yi wadanda suke ba da kofa wajen yi musu kutse, kamar sanya sauƙaƙƙun lambobin tsaro, da kuma sakaci wajen fito da bayanansu na sirri. Haƙiƙa ya kamata a san cewa lambar waya ma na daga cikin bayanan sirri.

Shawara: a san hikimomin mu’amala a yanar gizo

3. Hanyoyin Yaudara

Maha’inta kan bi hanyoyin da za su iya don yaudarar mutum ta yadda za a iya samun bayayansa cikin sauki. A kan tuntuɓi mutum a ƙafofoin sadarwa, kuma idan suka yi nasara sai ya ba su bayanan da hannunsa. Daga cikin irin waɗannan hanyoyin damfarar da ake yi mai suna Social Engineering akwai Smishing –wanda ya kasance hanya da madatsa kan bi don su samu damar cutar mutum ta hanyar tuntuɓarsa a waya da makamantansu. Haka nan a kan tura wa mutum likau ko wata manhaja da za ta iya zaƙulo bayanansa masu muhimmanci a cikin na’ura.

Shawara: wajibi ne a rinƙa kula da ingantaccen abu da jabu, musamman manhaja

Bayan duk waɗannan, tabbas ‘yan damfara suna amfani da ƙarfin iko wajen neman bayanan sirri mutum, wato su kan bi wasu hanyoyi keɓantattu da za su ba su damar cika ƙudiransu.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *