10

Dabarun Koyon Tsare-Tsaren Na’ura –‘Programming Language’ Ga ‘Yan Koyo

Tsare-tsaren na’ura, wanda aka fi sani da programming language wasu haɗe-haɗen haruffa ne, da lambobi, har da alamu; don ba wa na’ura damar yin wani keɓantaccen aiki a cikinta.

Akwai tsare-tsaren na’ura da dama da ake amfani da su wajen aiwatar da ayyuka a cikin na’ura kamar su Python, PHP, JavaScript, C# da sauransu. Ana amfani da su wajen ƙirƙirar manhajoji da shafukan yanar gizo da dama da aikinsu ya kasance wani keɓantacce.

Ma’abota tsare-tsaren na’ura, musamman ‘yan koyo suna fafutuka amma tare da samun matsala wajen tsara dabarun da suka dace waɗanda za a bi don koyon waɗannan yarukan na’uran. Don wannan dalilin aka fito da wasu hanyoyi na dabaru game da yadda za a tsara yanayin koyo da kuma bin shi daki-daki.

Waɗannan dabarun su ne kamar haka:

1. A zaɓi ɓangare

Mataki na farko da ya kamata a bi shi ne zaɓar ɓangaren da ya dace a koyi yaren na’ura don shi. A wani rubutu mai taken Yaya Ake Zama Developer’ an tattauna ɓangarorin ginin manhajar na’ura da waɗanda mutum zai zaɓa. Za a san cewa ɓangarorin na’ura suna da yawa, haka nan ɓangarorin da ya kamata a gina manhaja ko shafi ma suna da dama. Don haka abunda ya kamata shi ne zaɓar ɓangaren da mutum yake son tafiya a kai.

2. A ɗauki keɓantattun yarukan na’ura

Bayan an zaɓi ɓangare a nan kuma za a ɗauki keɓantattun programming languages da suka dace da ɓangaren. Misali, a ɓangaren gina manhaja ana amfani da yarukan na’ura kamar Java, C#, Python da makamantansu, don haka a nan sai mutum ya zaɓi wanne yare ne zai koya don dacewa da ƙudurinsa.

3. A tanadi kayan aiki

Haƙiƙa duk wani abu da za a fara sai da kayan aiki, don haka matakin farko da ya kamata a ɗauka a nan shi ne tanadar kayan aikin koyon wannan yaren da ake so a koya. Wato duk wani yare akwai wasu muhimman kayan aikin da ake amfani da su don gudanar da shi.

Misali haɗin manhaja da ake ƙira Integrated Development Environment (IDE) shi ne mai ba wa na’ura damar gudanar da wani yaren na’ura a cikinta, kamar dai manhajar XAMPP ko WAMP su ke tafiyar da yaren na’ura PHP da MySQL damar gudanarwa.

4. A tsara lokacin koyo

Abu mafi muhimmanci shi ne tsara lokacin koyo. Wato kamata ya yi a rubuta yanayin tsarin koyo a jadawali ta yadda za a sauƙaƙa koyon da kuma yadda za a ɓullo masa. Sau tari masana wannan harkar suna tsara abun nasu daki-daki kamar haka:

LanguageDurationProject
PHP3 Weekse-Library System
JavaScript2 WeeksUser Profile
Python5 WeeksCalculator

5. A rinƙa gwaji

Haƙiƙa duk wani mataki da ake bi a rayuwa sai da gwagwarmaya. A fannin na’ura ko fasaha abu ba ya yiwuwa ba tare da gwaji ba. Don haka duk wani mataki da aka je na koyo ya kamata a rinƙa gudanar da gwaji, ta wannan hanyar za a rinƙa fahimtar yadda abun yake a zahirance da kuma yadda za a rinka fuskantar ƙalubale a cikinsa –haka nan da yadda za a shawo kansu.

Ƙarin bincike: A nemi littafin Mohiddeen Ahmad mai suna ‘Program a Computer to Learn How to Think’ don sanin matakan da ya kamata a bi wajen sanin dabarun tsara koyon programming language da yadda za a fara.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

10 Comments

 1. Aamin ya saka da alkhairi yallabai, a ina zansamu shi wannan littafai “program a computer to learn how to think”?

 2. Muna godiya da wannan platform wato flowdiary ALLAH ya taimakemu baki ɗaya
  Nima Wannan semester zanyi wannan course wato computer 🖥️ programing
  CSC2401
  Muna godiya bloger ALLAH ya tallafi duk wani yunkuri na cigaban musulmi 🤲

 3. Masha Allah muna farin ciki sosai da gudunmawa dakake bayarwa

  Amma kamar yadda kace idan kanaso kazama kwarerren programmer dole saika tanadi kayan aiki shin kamar me yakamata mutum ya tanada Don koyon?

  Sannan kuma tayaya zan Samu Wannan littafi naka na “Program a computer to learn how to think”?

  • Godiya muke ranka shi dade. To kayan aikin dai ya danganta ga bangaren da mutum ya zaba, don haka suna da yawa kuma lokaci guda ba za a iya yanke hukunci a kai ba. Amma dai ka ci gaba da bibiyar mu a wannan shafi, za mu kawo bayanan dalla-dalla in Allah Ya yarda. Sannan za ka iya shiga nan domin sauke ,a href=’https://drive.google.com/file/d/16loYZLJ7_nh1Wmyhvia-vx-XcQpVpPIX/view?usp=sharing’>littafin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *