0

Nau’ukan Birrai nawa Ka Sani?

Biri na ɗaya daga cikin dabbobin da suke rayuwa a gari ko a daji, haka nan ya kasance dabba mafi baira a cikin dabbobi. Saboda wannan, masana da dama sun jingina asalin samuwar Ɗan’adam daga birrai –a wata nazariyya da ta yi ƙaurin suna a ƙarni na 19, wacce masanin kimiyyar halittu Charles Darwin ya gina a shekarar 1859.

Biri yana kamanceceniya da mutum sosai, masana bincike da likitoci suka ce ƙwayoyin halittarsa suna kama da na mutane da kaso 99%. Don wannan da wasu dalilai, biri ya kasance na daban a cikin sauran dabbobi ‘yan’uwansa.

Sai dai wasu lokutan mutane da dama suna samun matsala wajen gane bambance-bambancen da ke tsakaninsu, sakamakon kasantuwar nau’uka daban-daban a cikinsu.

Shin wane nau’i na biri ka sani kuma mene ne bayaninsa?

  • Masana suka ce akwai nau’ukan birrai sama da 260
  • An kasabta nau’ukan birrai zuwa gida biyu; New World da Old World
  • New World su ne waɗanda yawanci ke zaune a nahiyoyin America, su kuma Old World a nahiyoyin Asia da Africa
  • Birran Old World ba su da wutsiyar kirki, amma na New World ba su da
  • Ko mai karatu ya san biri mai suna Albert I ya taɓa zuwa sararin samaniya a shekarar 1949?
  • Ko an san biri yana son shan abunda zai bugar da shi?
  • Biri yana fahimtar ɗabi’un mutane kuma yana koya daga gare su

Wasu Nau’ukan Birrai

1. Capuchin Monkey

Irin waɗannan birran ana samunsu a nahiyar South America ko Central America. Tsayin wutsiyarsu ya kai inci 13-22, sannan suna kai wa aƙalla shekaru 10-15 suna raye. Capuchin Monkey yana daga cikin New World Monkey.

2. Marmoset Monkey

Marmoset Monkey ma suna daga cikin New World Monkey wanda ke zaune a Brazil, Columbia da Paraguay. Irin waɗannan birran ‘yan daidai, ba su da girma, don tsayinsu ba ya wuce sentimita 19. Wani abu game da su kuma shi ne suna yawan haihuwar tagwaye a kusan duk bayan watanni shida.

3. Tamarin Monkey

Birin Tamarin ɗan-ƙuƙub wanda ke kai shekaru aƙalla 15 yana raye. Haihuwarsu yana ɗaukar kwanaki 166, sannan suna da doguwar wutsiya.

4. Lion Tamarin

Irin waƙannan birran kuma masu kamanceceniya da zaki ta fuskar siffa, ana samun su a Brazil da maƙwabtansu. Saboda doguwar wutsiyarsu, tana kai wa inci 18. Shi ma wannan nau’in akwai wasu ƙananan nau’uka a ƙarƙashinsa kamar su Golden Lion Tamarin da Black Lion Tamarin.

5. Gorilla

A kan ƙira shi da goggon biri –yana daga cikin manyan nau’ukan birrai kuma munana. Ya kan iya kai wa shekaru 35-40 yana rayuwa. Nauyinsa ya kai kilogiram 160, tsayinsa kuma mita 1.6. Ya kan iya tafiyar kilomita 40 a sa’a guda.

Masana suka ce Gorilla yana da basira sosai, gwajin ma’aunin fiƙirarsa ya kai 75-95%, kamar yadda binciken BBC ya tabbatar a kan wani goggon biri, Koko, wanda yake gane yaren kurmanci.

6. Probiscis Monkey

Irin waɗannan birran masu dogon hanci suna daga cikin birrai da ake ƙira Old World Monkeys. Sun fi ƙwarewa wajen cin ciyawa da ‘ya’yan itatuwa. Tsayinsu yana kai wa sentimita 70, nauyi kuma kilogiram 20 (na namiji), mace kuma kilogiram 9.5

7. Baboons

Baboons ma suna daga cikin Old World Monkey. Haka nan su ma suna da wasu nau’uka a ƙarƙashinsu. Suna kai wa shekaru 35-45 suna rayuwa. Tsayinsu ya kai sentimita 70. Ana samunsu a wasu sassa a nahiyar Africa da wasu yankunan larabawa.

8. Mandrill Baboon

Mandrill yana daga cikin nau’ukan Baboon, su ma Old World Monkeys ne. Su kan iya rayuwa har tsawon shekaru 20.

9. Hamadryads Baboon

Ana samun birran Hamadryas Baboon a nahiyar Africa da wasu yankuna a kudu-maso-yammacin tsiribin larabawa –wanda aka fi sani da Arabian Peninsula. A kimiyyance ana ƙiransu Papio hamadryas.

10. Orangutan

Ana samun irin waɗannan birran a ƙasashen Indonesia da Malaysia. Su kan iya kai wa tsawon shekaru 35-45 suna rayuwa.

11. Macaque Monkey

Su kuma waɗannan sun fi zama a North Africa, nahiyar Asia da wasu wurare a yankin Gibraltar. A kimiyyance ana ƙiransu Macaca, suna kai wa tsayin sentimita 57.

12. Chimpanzee

Su kan rayu a nahiyar Africa su kai har tsawon shekaru aƙalla 35. Chimpanzee sun kasance daga cikin sanannun nau’ukan birrai a duniya. Suna da nauyin da ya kai kilogiram 40. Kamar dai sauran, su ma suna nuna kulawa ga ‘ya’yansu sosai.

13. Gibbon

A kan samu birran Gibbon a dazuzzakan gabashin Bangladesh, arewa-maso-gabashin India, kudancin China da kuma Indonesia. Masana suka ce waɗannan birran suna da murya sosai, don idan suka yi ƙara akan ji ko da ya kai tsayin kilomita guda.

Madogara:

[1]     Nayturr.com

[2]     MonkeyWorlds.com

[3]     Wikipedia.org

[4]     New Zoology

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *