0

Bayani Game da Tsibiri – ‘Island’ da Ire-irensa

tsibiri

Tsibiri, wato Island na nufin wasu yankuna da ke kan doron duniya waɗanda suka kasance ba sa haɗe da wata uwar nahiya, sa’annan kuma suna kewaye ne da manya-manyan ruwa wanda ya kasance teku.

Muhimman Bayanai Game Da Tsibiri

  • Tsibirin Java shi ne wanda ya fi tara yawan al’umma a doronsa, yawan mutanen da suke rayuwa a wannan tsibiri sun kai miliyan 130.
  • Tsauni mafi tsawo da ke kan tsibiri shi ne Puncal Jaya na tsibirin ƙasar New Guinea
  • Kaso ɗaya bisa shida – 1/6 na al’ummar duniya suna rayuwa ne a kan tsibirai
  • Greenland shi ne tsibiri mafi girma a duniya
  • Tsibirin Madagascar shi ne ya fi tara mabambantan halittun tsirrai da na dabbobi
  • Tsibirin Kansai wanda ke ƙasar Japan shi kuma Ɗan’adam ne ya gina shi wato Man-made Island.

Siffar tsibiri ta kan kasance babba ko ƙarama –islet sannan kuma shi tsibiri na iya kasancewa ƙasa mai zaman kanta kamar Madagascar, ko Mauritius ko Australia. Waɗannan su ne misalai na wasu tsibiran da suka kasance wata ƙasa ɗungurungum masu zaman kan su.

Baya ga wannan tsibiri na ɗauke da dukkan wata nau’in halitta a doronsa kamar yadda sauran nahiyoyi suke, wato ana samun dazuzzuka, dabbobi da ma hatittar Ɗan’adam. Haka nan tsibiri ya kasance wani dashi na duniya da ke cikin teku tsamo-tsamo; ana iya samun kogi, tapki, hamada, tsaunukan duwatsu da dai sauran su.

Yayin da aka haska tsibiri daga sararin samaniya wato satellite view za a hango shi ne kamar wata siffa ta dutse dake cikin ruwa wanda idan ya kusance kusa kuma za a ga yana canja siffa kamar wata nahiya, ha’ilau tsibiri yana dauke da nau’ukan kasa wadda mutun zai iya noma akan ta harma da gine-geni, hanyan abun hawa kamar su: tashar jirgin qasa da na sama da hanyar sauran kayan sufuri.

Jumullar sunan tsibiri ana ce masa Archipelago a turance. Don gane da batun ƙananun tsibirai su ma na da masu nau’in waɗanda suke cikin tekun ana ƙiran su islets sai kuma wanda ke samu a cikin kogi da tapki ana ƙiran su atolls

Ire-iren Tsibiri

Akwai nau’ukan tsibirai guda biyu da ake da su wanda suka bambanta ta hanyar da suke samuwa, su ne kamar haka:

1. Oceanic or Volcanic Island

Ire-ire ne na nau’ukan tsibiri wanda suke cikin sashen teku tsamo-tsamo, kuma sun samu ne sakamakon aman wuta da take kasan cewa a cikin teku har ta kai ga gina manya-manyan siffofin waɗannan tsibirai.

Masana kimiyya sun tabbatar da cewa ana ɗaukar lokaci mai tsawon gaske  kafin ire-iren tsibiran nan su samu har su kai ga lokacin da wata halitta za ta samu gurbin rayuwa akan su. Mafi yawan tsibiri da suka samu ta hanyar aman wuta sun jima da fara wanzuwa wanda har suka kai ga lokacin da dukkan wata halitta ke rayuwa akan su a mazannin matsugunen su. Irin wad’an nan irin tsibiran suna nan babu iyaka. Misalai:

i. Hawaii Island – ya kasance tsibiri a cikin sashen tekun Pacific ya kuma samu ne ta dalilin aman wuta.

ii. Philippines – Tsibirin ƙasar Philippines shi ma ya samu ne daga aman wuta kuma yana kudu-maso-gabashin nahiyar Asia ne, sa’annan yayi iyaka da sashinan teku gida biyu wato Celebes Sea da South East China

2. Continental Islands

Ire-iren waɗannan tsibiran suna da matuƙar bambanci da waɗanda su ke samuwa ta dalilin aman wuta. Wato su waɗannan irin nau’ukan tsibiran suna samuwa ne ta dalilin wani ɓangarewa da ake samu a jikin wata uwar nahiya a dai-dai lokacin aka samu rabewar farantan da doron ƙasa ke ɗauke a kai.

Haka nan su kan matsa gefe guda amma hakan yana faruwa ne cikin dubunnan shekaru tun lokacin da babu wanzuwar Ɗan’adam a doron duniya. Misalin ire-iren waɗannan tsibiran su ne kamar haka:

i. Green Island –wanda ya kasance tsibiri mafi girma a faɗin duniya wanda binciken masana ƙarƙashin ƙasa –geologists suka tabbatar da kasantuwarsa a nahiyar North America

ii. Madagascar Island –wannan ya kasance na huɗu a girma, haka nan wanda masana kan yi masa laƙabi da Red Island da ya kasantu a kudu-maso-gabashin nahiyar Africa

iii. Sri Lanka –shi ma muhimmin tsibiri ne da ke cikin tekun India. Bincike ya nuna cewa shi ma ya samu ne ta dalilin rabuwan farantan duniya wanda wata mashigan ruwa ta raba su da ƙaramar nahiyar India

Madogara
[1] Duckster.com
[2] Wikipedia.org
[3] World Atlas

Abdullahi Abubakar

Abdullahi Abubakar

I'm Abdullahi Abubakar from bajoga, gombe state. A former student in geography dept from fce,kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *