3

Yaya Siffofin ‘Hamada’ Suke?

hamada wato sahara

Cikin sauƙi, ‘Hamada’ wasu yankuna ne na duniya da suke da matuƙar zafin rana, bushewar ƙasa da ƙarancin ruwan sama wanda ba ya wuce sama da milimita 254 na damshi.

Sai dai ba lallai ba ne a ce yankin Hamada ya kasance mai zafi ba, don haka a nan dalilin kan iya zama kasantuwar nau’ukan Hamada da ake samun su a yankin da ake ƙira Poles –wato maƙurar arewaci ko kudancin duniya.

Dukkan yankunan Hamada na duniya sun ɗauki kaso ɗaya bisa uku (1/3) na faɗin duniya. Duk da kasancewa yankunan Hamada su na da yanayi na tsananin zafi, akwai wasu nau’ukan tsirrai da dabbobi masu ban sha’awa da ke rayuwa a wurin, kamar: dabbobi; macizai, kunamai, ƙadangare, ɓera, doki, raƙumi, barewa, jaki da dai sauransu, tsirrai; kuka, tsamiya, gawo, dabino, ƙarangiya, magarya da sauransu.

Karanta: Manyan Tekunan Duniya 5 Da Bayanansu

Bayanin da aka yi a sama shi ne kaɗan daga cikin siffofin Hamada, sannan kuma ga wasu daga cikin yankunan da Hamada kan kasantu a wurin:

1. Antarctic Desert
Wannan ita ce Hamada mafi girma a duniya kuma wacce ke kudancinta –South Pole a nahiyar Antarctica. Ta kasance Hamada da take samun wani kaso na damshi duba da inda ta ke tsugune a yankin mai matuƙar sanyi.

2. Sahara Desert
Wannan yankin Hamadar ya kasance wani sashi na nahiyar North Africa wanda girmanta ya kai nahiyar Europe ko ƙasar America. Kalmar Sahara ta samu ne daga harshen larabci wadda take nufin “tarin yashi/rairaiyi” wanda tsayin sa ya kai murabin ƙafa 500 na tsayi. Ƙasashen da ke Hamadar Sahara sun haɗa da Libya, Algeria, Tunisia, North Sudan, Egypt, Morocco da kuma wani sashi na kasar Niger daga kudancin ta.

3. Arabian Desert
Wannan yanki na Hamada na zaune ne a yankin da ake ƙira gabas ta tsakiya wanda ya mamaye ƙasashe irin su Saudi Arabia, Qatar, Kuwait, Yemen, Oman, Syria, Iraq da UEA. Sannan ya kasance yanki na biyu mafi zafin rana bayan yankin Sahara, wasu lokutan ana ƙiran yankin Rab’ul Khali wanda ya zamo cibiya mafi girma a wajen samar da ɗanyen mai –Crude Oil a duniya baki ɗaya.

Karanta: Bayani Game da Nahiyoyin Duniyar Earth

4. Kalahari Desert
Kalahari Desert yana kudancin Africa wanda ya mamaye wasu ƙasashe kamar su Namibia da Botswana. A ita wannan hamadar yanayi yana faruwa ne cikin ban al’ajabi, dalili kuwa shi ne cikin dare yanayi na low temperature yana iya sauƙa zuwa 0̊ C kuma lokacin rana ya na iya kai wa 40̊C. Yankin na Kalahari ya kasance mai ban sha’awa duba da yadda yake da nau’ukan dabbobin daji masu yawan gaske.


5. Gobi Desert
Ita wannan hamadar ta na tsakanin arewacin kasar China da kudancin Mongolia wacce a tarihi ta kasance wani sashi na babbar daular Mongol. Kuma shi wannan yanki ya kasance hamada mai sanyi ce saboda yankin yana kan tsaunukan duwatsu wanda ya sa yankin ya kai murabin ƙafa 300 daga matakin ƙasa.

Madogara
[1] Duckster.com
[2] Desertusa.com
[3] Encyclopedia of Earth and Science

Abdullahi Abubakar

Abdullahi Abubakar

I'm Abdullahi Abubakar from bajoga, gombe state. A former student in geography dept from fce,kano

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *