3

Manyan Tekunan Duniya 5 Da Bayanansu

Duk da teku –wato ocean ya kasance mai amfani ga dukkanin wani lungu da saƙo na duniyar nan, amma akwai wasu abubuwan dubawa a tattare da shi wanda mutane za su so sani.

  • Ruwa ne ya mamaye kusan kaso 71% na faɗin duniya
  • Ruwan teku yana da guba, don haka ba a shan sa
  • Akwai manyan tekuna 5 a duniya

Daga cikin amfanin teku akwai zirga-zirgar kaya da ake yi daga wata ƙasa zuwa wata –ana safarar kayayyaki ta hanyar jirgin ruwan. Hakan ya kasance mafi sauƙi duk da yana ɗaukar lokaci kafin ya isa wata ƙasa.

A cikin manyan tekunan duniya akwai waɗannan waɗanda suka yi fice fiye da sauran, kuma suke da faɗin gaske.

1. Pacific Ocean

Tekun Pacific shi ne teku mafi girma a duniya wanda ya mamaye kusan kaso 30% na dukkanin faɗin duniyar. Masana suka ce kusan rabin ruwan da ke wannan duniyar a tekun Pacific yake. Zurfinsa ya kai mita 11,022 sannan faɗin inda ya mamaye kuma ya kai 165.2 million km^². Tekun Pacific yana tsakanin nahiyoyin America da kuma Australia da Asia.

2. Atlantic Ocean

Mutane da dama suna tunanin Atlantic Ocean –wanda aka fi sani da Tekun Atlantika shi ne mafi girma a duniya, amma sai dai a zahirin kuma shi ne na biyu bayan Tekun Pacific. Wannan tekun yana tsakanin nahiyoyin America da Europe da Africa. Shi ma zurfinsa ya kai mita 8,486 sannan faɗin inda ya mamaye kuma ya kai 106,460,000 km^².

3. Indian Ocean

Teku na uku mafi girma a duniya shi ne Indian Ocean. Masana binciken teku da abunda ke cikinsa suka ce wanann tekun ya ƙunshi aƙalla kaso 20% na dukkanin ruwan da ke duniyar earth. Tekun yana makwabtaka da India, da nahiyar Africa, da Australia, da kuma wani teku da za a gani nan gaba mai suna Southern Ocean. Bugu da ƙari kuma tekun yana gugar wasu manyan farantin duniya.

4. Southern Ocean

Sai dai mutane ba su cika lura da wannan tekun ba, kasancewarsa a nesa da ƙasashen mutane –saboda yana maƙwabtaka da nahiyar Antarctica; wacce babu halittu masu rai a ciki, sai dai ko na bincike. Zurfin tekun ya kai mita 4,000, sannan shi ne ya mamaye kaso 6% na duniyar earth.

5. Arctic Ocean

Tekun Arctic shi ne mafi ƙanƙanta daga cikin manyan tekunan duniya guda 5. Duk da haka zurfinsa ya kai mita 1,038, sannan yanayin zafi da sanyinsa kuma -2^̊C ne. kamar dai Southern Ocean, shi ma mutane ba su cuka zuwa ba –ko da yawon buɗe-ido.

Madogara:

[1] Encyclopedia of Earth Science

[2] Encyclopedia Britannica

[3] National Geographic

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *