11

Bayani Game da Nahiyoyin Duniyar Earth

Nahiya –wato continent na ɗaya daga cikin manya-manyan sashinan doron ƙasa da dukkan wata halitta ke rayuwa a kai, wanda ya ƙunshi tsirrai da dabbobi haɗe da abubuwa marasa rai kamar tsaunuka da duwatsu.

Doron ƙasa a wannan duniyar tamu wato Earth ta na da nahiyoyi guda bakwai tare da wasu ƙananan tsibirai da suke tattare da waɗannan manyan nahiyoyin. Sannan abu muhimmi da mai karatu zai sani shi ne doron ƙasa yana ƙunshe da kado 29 na wannan duniyar, wanda sauran ragowar duk ruwa ne wato teku.

Karanta: Bayani A Kan Farantan Duniya – ‘Tectonic Plates’

Waɗannan nahiyoyin da muke da su sune:

1. Asia
Wannan nahiya ita ce mafi girman faɗin ƙasa a cikin dukkan nahiyoyin duniya wacce ƙunshi kaso 60 na yawan al’ummar duniya. Bisa ƙididdiga na masana suka ce yanzu yawan mutane a wannan nahiya ya kai 3,879,000,000.

Nahiyar ta yi iyaka da nahiyar Europe daga sashin yamma, daga gabas kuma tana da iyaka da tekun Pacific, san nan kuma sai tekun India daga kudu, sai kuma tekun Arctic daga arewa.

2. Africa
Nahiyar Africa ita ce ta biyu a girma bayan Asia, hakanan ita ce ta biyu a yawan al’umma a inda take da kaso 14 na yawan al’ummar duniya –wato adadinsu ya kai 922,010,000. Ta na da yawan ƙasashen da suka kai aƙalla 54.

Sannan nahiyar Africa tana kewaye da manyan sashinan tekunan duniya kamar su tekun Mediterranean wanda ya kasance sashi na tekun Atlantic daga arewa da yammacin nahiyar, kuma daga kudu zuwa gabas kuma tekun India ne yake kewaye da ita da wani sashi na tekun Maliya wato Red Sea a turance.

3. North America
Wannan nahiyar ita ce ta uku a girman faɗin ƙasa, sannan kuma ta hud’u a yawan al’ummar da ke rayuwa a kanta waɗanda suka kai yawan 528,720,588. Nahiyar North America ta na da ƙasashe 31 sannan ta yi iyaka da tekun Atlantic daga gabas, daga yamma kuma tekun Pacific, daga arewa kuma ta na da iyaka da tekun Caribbean.

4. South America
Ana mata lakabi da tagwayen North America –saboda kasancewarsu a kusan yanki guda na America. Ta kasance ta huɗu a girman ƙasa, sannan ta na da kaso 6 na yawan al’ummar da ke rayuwa waɗanda yawan su ya kai 382,000,000. Hakanan ta ƙunshi ƙasashe 15 kacal, kuma tana kewaye da tekun Atlantic daga arewa da gabashin ta, sai kuma tekun Pacific daga yamma da kuma tekun Caribbean daga arewa-maso-gabas.


5. Australia
Wannar nahiya ta ƙunshi babban doron ƙasa na ƙasar Australia da wasu muhimman tsibirai kamar su New Genuine da Tasmanian. Yawan al’ummar da ke rayuwa a wannar nahiya ya kai adadin mutum 22,000,000. Nahiyar Australia tana kewaye da mabambantan tekuna kamar su Timor, da Arafura da mashigan ruwan Torres daga sashin gabas, da kuma tekun Coral da Tasman daga yammaci, daga yamma zuwa kudu kuma ta yi iyaka da tekun India

6. Europe
Nahiyar Turai ita ce ta biyu a mafi ƙanƙanta, sannan ta uku a yawan al’ummar da ke rayuwa a duniya saboda ta ƙunshe kaso 11 na yawan al’ummar duniya waɗanda suka ka kai yawan 731,000,000. Nahiyar Turai ta yi iyaka da tekun Atlantic daga yamma, sai tekun Mediterranean daga kudu, sai tekun Arctic daga gabas. Sai kuma muhimmin iyakar ta da Asia wanda tsaunukan Ural su ka raba su

7. Antarctica
Wannan ita ce nahiya ta biyar a girman ƙasa wacce ta ke tsugune a maƙurar kudancin duniya, sai dai ita ce mafi ƙanƙanta a yawan al’ummar da ke rayuwa a cikinta. Mafi yawan mutanen da ke rayuwa a cikinta ma’abota bincike ne na sararin samaniya da na ƙarƙashin ƙasa; ita ce nahiya mafi sanyi, iska, da bushewa. Saboda sanyi, tana yawan zubar da dusar ƙanƙara. Nahiyar tana kewaye da tekun kudancin duniya ne baki ɗaya.

Karanta: Wasu Sanannun Zumɓutan Doron ƙasa 8 da Muhimman Bayanai Game da Su

Madogara
[1] Encyclopedia of Earth and Science
[2] Country Hand Book
[3] Wikipedia.org

Abdullahi Abubakar

Abdullahi Abubakar

I'm Abdullahi Abubakar from bajoga, gombe state. A former student in geography dept from fce,kano

11 Comments

  1. Masha Allah. Amma nataba jin wani yana fada cewa ita Nahiyar Antarctica Dabbobine acikinta ba mutane ba.

  2. Allah yakara basira kuma kuna birgemu sosai daga masoyin ku BUHARI MUHAMMAD KAFIN FULANI GWARAM LGA JIGAWA STATE Student at fce t gombe maths/computer department dan ALLAH inaso number ka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *