4

‘Cloud Computing’ Ba Gajimare Yake Nufi Ba!

Cloud Computing na nufin ƙirƙira da amfani da wasu sauƙaƙƙun hanyoyi don adana bayanai a yanar gizo maimakon adana su a ƙananan rumbunansu a cikin na’ura.

Sau tari mutane da dama, musamman waɗanda ba su danganci harkar na’ura da yanar gizo ba, suna tunanin wannan fiƙira ko tsarin Cloud Computing na nufin mu’amalar na’ura da gajimare ko girgije, sai dai lamarin ba haka yake ba.

Karanta: Bayani kan Quantum Computer: Tsari, Amfani da Tasirinta a Duniyar Zamani

A baya da aka kasance ana amfani da ƙananan rumbunan bayanai don adana bayanai kafin wanzuwar yanar gizo babu wata hanyar adana bayanai da za a iya amfani da su zuwa nan gaba, wato babu mafi ingancin tsarin Cloud Computing.

Karanta: Yanar Gizo: Bayani da Bambanci Tsakanin Surface Web, Deep Web da Dark Web

Amma a yau, sakamakon zuwan yanar gizo, wannan tsari na adana bayanai a rumbunan bayanai da ke kan yanar gizo ya ba wa mutane damar shigarsu da kula da su duk inda suke a faɗin duniya.

Karanta: Bambancin ‘Web’ da ‘Internet’: Bayani kan Ma’anonin PAN, LAN, MAN da WAN

Wani babban cigaba da tsarin Cloud Computing ya kawo shi ne yadda mutum zai iya adana bayanansa a kan yanar gizo kuma ya shige su duk lokacin da yake so, a kowacce irin na’ura kuma a duk inda yake a cikin duniyar nan. Don haka wannan tsarin ya ba wa masana damar adana muhimman bayanai da suke gudun baɓan su, ko kuma adana su don sirri.

Amfanin Cloud Computing

Daga cikin amfanin Cloud Computing akwai:

1. Tafiya da zamani

2. Rashin tsada

3. Boye bayanai don kutse

4. Sauƙin amfani

5. Dawo da bayanin da suka ɓata

6. Ƙarin ma’ajiya

7. Tsaro

Karanta: Hikimar Rumbun Bayanai – ‘Database’ da Amfaninsa a Duniyar Zamani

Daga cikin misalan Cloud Computing kuwa akwai Google Drive, Apple iCloud, Dropbox da sauran waɗanda a kan iya adana bidiyoyi, imel, manhajoji da makamantansu. Duk waɗannan manhajoji ana amfani da su wajen adana bayanai a kan yanar gizo, wanda ba sai mutum ya yi amfani da ma’ajiyin na’urarsa ba.

Binciken gidauniyar Synergy Research Group ya tabbatar cewa manyan kamfanoni 4 suke ɗauke da kaso 67% na bayanan da ke Cloud Computing su ne Amazon Web Services, Azure, Google Cloud da kuma Alibaba Cloud.

Ire-Iren Cloud Computing

1. Private Cloud –wannan tsari ne yadda kamfani ne kaɗai zai iya amfani da ma’ajiyarsa don adana bayanansa. Wannan tsarin shi yake kama da yadda ake adana bayanai a ma’ajiyar na’urori.

2. Public Cloud –wannan tsarin kuma wani kamfani ne na musamman wanda ya samar da ma’ajiyar zai kula da duk wani yanayi na tafiyar da ma’ajiyar.

3. Hybrid Cloud –wannan kuma shi ya haɗa Public Cloud da Private Cloud. A nan, a kan iya musayar bayanai tsakanin kamfanoni ko manhajojin da ke aiki da waɗannan tsaruka.

Matakan Cloud Computing

1. Software-as-a-service –wannan mataki ne Cloud Computing a inda kamfanonin da ke da alhakin samar da ma’ajiyu za su ba wa mutane manhajojin da za su iya amfani da su wajen sarrafa ma’ajiyarsu. Misalin irin waɗannan su ne Microsoft Office 365.

2. Infrastructure-as-a-service –shi kuma wannan shi ke bayar da duk wasu abubuwa da za a buƙata a tafiyar da ma’ajiyar bayanai, kamar tsarin na’urori, manhajar kanta da sauransu.

3. Platform-as-a-service –a wannan matakin kuma ake tsara aikin masana tsare-tsare, yanayin aikin da ƙayatarwa, tsaro, tsaruka, na’urori da makamantansu don tabbatar da dacewar wannan ma’ajiya.

Tsarin Cloud Computing

Matakai biyu a tsarin Cloud Computing su ne front-end da back-end, waɗanda daman suka kasance a matakan ƙirƙirar manhajoji ko shafuka.

Abunda aka nuna a nan shi ne; abu na farko da ake yi shi ne shiga manhajar shiga yanar gizo don kusantar ma’ajiyar bayanan nan, daga nan kuma sai amfani da manhajar da ke kusanci da ma’ajiyar don ba da damar shiga ma’ajiyar.

Madogara

[1]     InfoWorld.com

[2]     Wikipedia.org

[3]     Microsoft.com

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *