4

Dabarar Datsa – ‘Smishing’ Da Yadda Ake Yinta

Wata dabarar datsa da ta yi ƙaurin suna a wannan lokacin da ake ƙira smishing ta sanya mutane da dama a halin ha’ula’i, duba da yadda ake yaudararsu don cutar da su.

Smishing wata dabarar kutse ce da ‘yan datsa –waɗanda aka fi sani da hackers su ke amfani da ita wajen yaudarar mutane. Suna amfani da wannan dabarar ne wajen yaudarar mutane ta hanyar tura musu saƙonni ana tambayarsu game da waɗansu bayanansu na sirri.

Karanta: Wasu Shawarwari akan Tsaron Na’ura

Irin wannan kutsen yana daga cikin ire-iren kutsen social engineering da ya addabi mutane. Don haka mutane da dama suna yawan ƙorafe-ƙorafe akan yadda ake cin su da yaƙi ta hanyar shiga asusansu ba tare da saninsu ba.

Karanta: Muhimman Hanyoyi 5 Don Kare Wayar ‘Android’ Daga Annobar Na’ura Da Kutse

Sai dai duk da haka, abunda ba a sani ba shi ne, mutane su ke ba da damar yi musu kutse da kansu, saboda su suka kasance masu bayar da bayanansu da hannusu.

Ko Yaya Ake Wannan Kutse?

Hanya mafi sauƙi da madatsa kan bi wajen ruɗar mutane ita ce tura musu saƙonni, musamman zuwa asusun saƙonninsu na waya da ke nuna kamar saƙon yana da inganci, misali; saƙo daga 500, ko 424 ko makamancin haka.

Karanta: Shawarwari 5 Don Laƙantar Tsaron Na’ura da Asusai

Irin waɗannan saƙonnin suna tunzura mutum ya bayar da bayanansa na sirri, musamman idan aka dubi lambobin da aka yi amfani da su wajen tura saƙonnin. Ta wannan hanyar mutum zai yi tunanin daga wani kamfani ne ake neman bayanansa.

Kamanceceniyar Kalmomi

Akwai wasu kalmomi da suke kamanceceniya da smishing, waɗanda duk suka kasance ire-iren dabarar kutse Social Engineering.

Smishing  PhishingVishing
Tura saƙonni zuwa asusun saƙonnin waya don ruɗar da mutane tura bayanansu na sirri zuwa ga madatsaTura wa mutane likau, manhajoji ko saƙonnin imel don karɓar wasu muhimman bayanansu na sirriƘiran mutane a waya ta hanyar bi da lallami da kalaman yaudara don damfararsu, musamman don samu bayanansu na sirri

Yaya Mutum Zai Kare Kansa?

1. Kada a danna likau ko shafin yanar gizon da ba a yarda da su ba

2. Kada a mayar da martani ga saƙon imel ɗin da ba a yarda da shi kuma ba a san wanda ya turo shi ba

3. Kada a kula da ƙiraye-ƙirayen wayoyin da ba a san su ba

4. A rinƙa kula da shafukan da ake ziyarta da tabbatar da sahihancinsu

5. Kada a sanya manhajar da ba a tabbatar da sahihancinta cikin na’ura ba

6. A kula da saƙonni a cikin waya kuma kada a mayar da martani gare su.

Tabbas ya zama wajibi a kula da waɗannan shawarwari don kada a yi nadama nan gaba, domin yanzu kutse ya zama ruwan dare a wannan zamani. Bugu da ƙari, a rinƙa kula da saƙonnin da ake samu daga banki –haƙiƙa ba kowane saƙo ba ne daga asusun banki, sau tari ana iya amfani da wasu dabaru don kutse ciki na’urori don tura wa mutane saƙonnin bogi.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *